Ranar ‘Yancin Kai: Tinubu zai yi jawabin ƙasa ƙarfe 7 na safiyar Alhamis

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai yi wa al’ummar ƙasa jawabi a safiyar ranar Alhamis, 1 ga Satumba, 2026 yayin da Nijeriya take cika shekaru 66 da samun ‘yancin kai.

A cewar Kakakinsa Bayo Onanuga, Shugaban zai gabatar da jawabin ne da misalin ƙarfe 7 na safe a matsayin wani ɓangare na muhimman al’amuran da za a gudanar a ranar.

Onanuga, wanda ya bayyana haka a wata sanarwa a ranar Laraba, ya shawarci dukkan gidajen yaɗa labarai da su haɗe da gidan talabijin na NTA da gidan rediyo na Federal Radio Corporation of Nigeria wajen yaɗa saƙon shugaban kai-tsaye.

A halin yanzu dai Shugaban yana Legas, inda daga can ne ake tsammanin ya gudanar da muhimmin bikin ranar samun ‘yancin kan Nijeriyar.

By Babaji

Leave a Reply