Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatinsa ta biya kusan Naira biliyan 32 daga cikin bashin giratuti da sauran haƙƙoƙin da suka taru na ma’aikatan da suka yi ritaya, wanda ya gada daga tsohuwar gwamnati da ya kai Naira biliyan 48.
Gwamna Yusuf ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a jawabinsa yayin bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Najeriya, wanda aka gudanar a filin wasanni na cikin gida na Sani Abacha da ke Kano.
Ya ce gwamnatin jihar ta kuma ci gaba da biyan fansho a kan kari a kowane wata, tare da sake duba mafi ƙarancin fansho na wata-wata daga Naira 5,000 zuwa Naira 20,000.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da bai wa jin daɗin ma’aikata da ‘yan fansho muhimmanci ta hanyar biyan albashi a kan lokaci, inganta tsarin albashi da ɗaukar matakan ƙarfafa ma’aikatan gwamnati.
A cewarsa, Jihar Kano ta ci gaba da biyan ma’aikata albashi na
kafin ko a ranar 25 ga kowane wata, yayin da take aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 71,000 ga ma’aikatan gwamnati.
Gwamna Yusuf ya kuma ce gwamnatin jihar na ɗaukar nauyin ma’aikatan gwamnati domin samun ƙarin horo na ƙwarewa, ciki har da shirye-shiryen horaswa a kwalejin koyar da ma’aikatan gudanarwa ta Najeriya (ASCON), domin bunƙasa ƙwarewarsu a fannin gudanarwa da jagoranci.
Kazalika, ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na samar da ƙwararrun ma’aikata masu ƙwazo, waɗanda za su iya gudanar da ayyukan gwamnati yadda ya kamata.
Gwamnan ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na gina ma’aikata masu ƙwarewa da kishin aiki, tare da tabbatar da cewa an san irin gudunmawar da ma’aikatan da ke aiki da waɗanda suka yi ritaya suka bayar, kuma ana mutunta haƙƙoƙinsu cikin mutunci.
