An tsinci gawar dagaci a rami bayan sace shi a Kano

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

An ruwaito cewa an kashe dagacin ƙauyen Aujarawar Alƙali da ke ƙaramar Hukumar Gezawa a Jihar Kano, Alhaji Ahmad Yakubu Ahmad, bayan da waɗanda suka yi garkuwa da shi suka kashe shi.

An yi garkuwa da Ahmad ne a ranar 17 ga Satumba, 2026, lokacin da wasu ’yan bindiga suka mamaye al’ummar yankin da daddare tare da tafi da shi.

Daga bisani, an gano gawarsa a wani kabari mara zurfi a ƙauyen Danladin Gezawa, bayan da mazauna yankin suka gano wurin da aka binne shi.

An gudanar da sallar jana’izarsa da misalin ƙarfe 3 na rana a ranar Laraba, kafin a binne shi.

Musa Garba, wani mazaunin Gezawa, ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu ta wayar tarho.

A cewarsa, maharan sun azabtar da dagacin har suka kashe shi, inda suka yanke masa ƙafa ɗaya sannan suka ɗaure hannuwansa a bayansa.

Garba ya ce, “Na halarci sallar jana’izarsa a yau Laraba da misalin ƙarfe 3 na rana. Maharan sun azabtar da dagacin har suka kashe shi, inda suka yanke masa ƙafa ɗaya tare da ɗaure hannunsa a bayansa. Sun ci gaba da gallaza masa har sai da ya mutu.

“Bayan mutuwarsa, waɗanda suka yi garkuwa da shi sun binne gawarsa a wani kabari mara zurfi a wani ƙauye mai suna Danladin Gezawa. Bayan kwanaki huɗu, wasu mazauna ƙauyen suka gano kabarin tare da sanar da sauran jama’a.”

Garba ya ƙara da cewa matar marigayin ce ta gane gawar mijinta bayan an gano ta, sannan aka kai gawar zuwa asibiti domin tabbatar da mutuwarsa.

Ya ce, “Gawar ta riga ta fara lalacewa lokacin da aka gano ta. An kai ta asibiti, inda aka tabbatar da cewa ya mutu, sannan aka binne shi daga bisani.”

Har zuwa lokacin da aka wallafa rahoton, rundunar ’yan sandan Jihar Kano ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.

By ukarofi

Leave a Reply