Mambila: Lauyoyi sun nemi a binciki Malami kan zargin rashin ɗa’a

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

ƙungiyar Society of Public Interest Lawyers in Nigeria (SPI-LAW) ta buƙaci Kwamitin Ladabtar da Lauyoyi (LPDC) na Body of Benchers da ya fara binciken tsohon Antoni-Janar na Tarayya kuma tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN, kan zargin aikata rashin ɗa’a da kuma abin da ƙungiyar ta ce ya saɓa wa ƙa’idojin aikin lauya.

ƙungiyar ta shigar da ƙorafi a gaban LPDC bisa wasu bayanai da kuma hukuncin Kotun Sasanta Rikice-rikice ta International Chamber of Commerce (ICC) kan yadda aka tafiyar da batun aikin samar da wutar lantarki na Mambilla a Jihar Taraba.

A ranar 17 ga Satumba, 2026, wata kotun sasanta rikice-rikice ƙarƙashin ICC da ke Paris ta yi watsi da ƙarar Sunrise Power and Transmission Company Limited da ta nemi a biya ta kuɗaɗe masu yawa dangane da rikicin aikin Mambilla. Hukuncin ya kuma ƙunshi suka kan yadda aka tafiyar da wasu yarjejeniyoyin da suka shafi rikicin.

SPI-LAW ta ce wasu daga cikin abubuwan da kotun ta bayyana sun haifar da buƙatar a binciki rawar da Malami ya taka a lokacin da yake Antoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a.

ƙungiyar ta ce zarge-zargen sun shafi mutuncin aikin lauya da kuma amincewar jama’a ga masu gudanar da wannan sana’a, don haka ta bukaci LPDC ta gayyaci Malami domin ya samu damar amsa zarge-zargen da ake yi masa bisa tsarin doka.

Sai dai Malami ya musanta zargin cewa ya yi aiki ba tare da kishin ƙasa ba, inda ya ce duk matakan da ya ɗauka a lokacin sun kasance ne domin kare muradun Nijeriya da kuma neman warware doguwar takaddamar da ta shafi aikin Mambilla. Ya kuma ce babu wata hujja da aka gabatar da ta nuna cewa ya samu wata fa’ida ta kuɗi daga yarjejeniyar.

SPI-LAW ta jaddada cewa zarge-zargen da aka yi wa Malami ba hukunci ba ne, tana mai cewa ya kamata a ba shi cikakkiyar damar kare kansa tare da tabbatar da adalci kafin a yanke wani hukunci a kansa.

Yanzu haka ƙorafin na gaban LPDC, inda ake sa ran kwamitin zai bi matakan da suka dace wajen duba zarge-zargen da ƙungiyar ta gabatar da kuma martanin Malami kafin ɗaukar matakin da ya dace.

By ukarofi

Leave a Reply