Siyasa da son zuciya ne suka hana aiwatar da shari’ar Musulunci — Kwamitin tabbatar da adalci

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Kwamitin Tabbatar da Adalci a cikin Al’umma, ƙarƙashin shugabancin Malam Ilyasu ɗorayi, tare da Sakataren Kwamitin, Malam Rabi’u, da Mataimakin Sakataren, Ustaz Muhammad Bello Ibrahim, sun bayyana cewa akwai dalilai da dama da suka hana aiwatar da Shari’ar Musulunci yadda ya kamata a wasu jihohin Nijeriya da suka fara aiwatar da ita tun shekarar 1999, musamman a jihohin Arewa.

Sun bayyana hakan ne a yayin wani taron gangamin malamai daga ƙungiyoyi da ɗariku daban-daban, ciki har da waɗanda ba sa cikin wata ɗariƙa, wanda aka gudanar ranar Lahadi a Makarantar Nazarin Harshen Larabci da ke Kano.

Shugaban da sakatarorin kwamitin sun bayyana matsayinsu ne a jawabai daban-daban a wajen taron, wanda aka yi wa taken “Mu Haɗu Mu Dawo da Shari’a a Kan Gaba”, inda suka yi waiwaye kan irin ƙoƙarin da wasu malamai suka yi a baya wajen ganin an aiwatar da Shari’ar Musulunci yadda ya kamata.

Sun ambaci malamai irin su Malam Umar Sani Fagge, marigayi Malam Yahya Faruku Chiɗe, Malam Yahya Tanko, Alhaji Ado Muhammad na Freedom Radio da sauran malamai da suka yi irin wannan yunƙuri. Sun ce wasu daga cikinsu sun rasu, yayin da wasu ke nan da ransu, amma an gayyaci su domin a haɗa kai ba tare da la’akari da bambancin ɗarika ba, bisa manufar “a gudu tare, a tsira tare”.

A cewar kwamitin, Shari’ar Musulunci ta shafi dukkan wanda ya furta Kalmar Shahada, kuma suna ganin Musulmi na buƙatar aiwatar da ita saboda amfanin da suka ce za ta kawo masa a duniya da lahira. Sun kuma bayyana cewa rashin aiwatar da ita na iya zama asara ga Musulmi a duniya da lahira.

A ƙarshe, Malam Rabi’u da Malam Muhammad Bello Ibrahim sun jaddada cewa dawo da aiwatar da Shari’ar Musulunci na buƙatar haɗin kan Musulmi, inda suka danganta matsayinsu da umarnin Allah ga Musulmi da su riƙe igiyarsa baki ɗaya, kada su rarrabu.

Sun ce a fahimtarsu, haɗin kai shi ne tushen samun ci gaba, yayin da son zuciya da siyasa suke daga cikin abubuwan da suka kawo cikas ga cikakken aiwatar da Shari’a, musamman a wasu jihohin Arewacin Nijeriya.

Sun kuma danganta wasu daga cikin matsalolin da suke addabar ƙasar, ciki har da matsalolin tattalin arziki da rashin tsaro, da abin da suka kira gazawar tsarin mulki na zamani wajen warware matsalolin al’umma. Sun bayyana cewa a ra’ayinsu, babu mafita sai ta hanyar aiwatar da Shari’ar Musulunci.

By ukarofi