Tun 1984 da Sarkin Gumel ba ni kyauta a FGC Kano ya shiga raina — Dr Muhammad Musa

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Dakta Muhammad Musa Muhammad, Shugaban ƙungiyar ƙwararrun Likitoci ta Jihar Jigawa kuma Shugaban Sashen Fida na Asibitin Koyarwa na Rashid Shekoni da ke Jihar Jigawa, ya bayyana marigayi Sarkin Gumel, Alhaji Ahmad Muhammad Sani na Biyu, a matsayin dattijo na gari, uba kuma jagora wanda ya yi tasiri sosai a rayuwarsa.

Dr Muhammad Musa ya ce marigayi Sarkin Gumel ya shiga cikin rayuwarsa tun shekarar 1984, lokacin da ya ba shi wata kyauta da hukumar Federal Government College Kano ta ba shi sakamakon nuna ƙwazo da Ubangiji ya ba shi damar yi a lokacin da yake ɗalibi a makarantar.

Ya bayyana cewa wannan kyauta da marigayi Sarkin Gumel ya ba shi ta yi masa tasiri sosai, har ta shiga cikin abubuwan da ba zai manta da su ba a rayuwarsa.

Haka kuma, ya ce Jihar Jigawa, Arewa da Nijeriya baki ɗaya sun yi rashin sarki adali, mai tausayi, kyakkyawar mu’amala da sanin ya kamata, wanda baya raina ko wulaƙanta wani mutum.

A cewarsa, suna kallon marigayi Sarkin Gumel a matsayin malami kuma abin koyi a duk inda mutum ya samu kansa, musamman wajen shugabanci da sauran harkokin zamantakewa.

Ya ce marigayi Sarkin Gumel mutum ne mai tsoron Allah, taƙawa da kyawawan ɗabi’u, waɗanda suka dace da koyarwar Manzon Allah (SAW), musamman wajen kyautata mu’amala da mutane.

Da yake magana kan cikar Jihar Jigawa shekaru 35 da kafuwarta, Shugaban Sashen Fida na Asibitin Koyarwa na Rashid Shekoni, kuma babban likitan fida, Dr Muhammad Musa Muhammad, ya bayyana cewa jihar ta samu ci gaba mai tarin yawa tun daga lokacin da aka ƙirƙire ta.

Ya ce ɗaya daga cikin fannonin da aka samu ci gaba sosai shi ne harkar kiwon lafiya, inda aka gina manyan asibitoci, cibiyoyin lafiya da makarantu da cibiyoyin koyar da aikin lafiya a sassa daban-daban na jihar.

A cewarsa, wannan babban ci gaba ne da Jihar Jigawa ta samu tun daga gwamnatocin da suka gabata har zuwa gwamnatin yanzu ta Malam Umar Namadi, musamman yadda aka samu kyakkyawan yanayi da kulawa ta musamman a fannin kiwon lafiya da sauran fannoni na ci gaban al’umma.

Dr Muhammad Musa ya ƙara da cewa wannan kyakkyawan yanayi ya sa likitoci daga jihohin makwabta da sauran wurare ke sha’awar zuwa Jihar Jigawa domin yin aiki idan suka samu dama ko wata kafa da za ta ba su damar yin hakan.

Ya ce wannan ba ƙaramin lamari ba ne, domin yana nuna irin ingancin yanayin aiki da aka samu a fannin kiwon lafiya a jihar.

Ya bayyana cewa idan aka kwatanta da shekarun baya, lokacin da adadin ƙwararrun likitocin jihar bai kai biyar ba, yanzu ana iya samun ƙwararrun likitoci sama da 40 da suka kware a fannoni daban-daban.

A cewarsa, wannan ƙaruwa a yawan ƙwararrun likitoci na daga cikin alamomin ci gaban da Jihar Jigawa ta samu a fannin kiwon lafiya cikin shekaru 35 da kafuwarta.

By ukarofi