Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Ɗan majalisar da ke wakiltar mazaɓar tarayya ta Birnin Magaji/Kaura Namoda a jihar Zamfara, Hon. Aminu Sani Jaji, ya ce duk da ƙalubalen tattalin arziki da ƙasar ke fuskanta, jam’iyyar All Progressives Congress (APC) har yanzu tana da goyon baya mai yawa a tsakanin al’ummar jihar Zamfara.
Hon. Jaji ya bayyana hakan ne a Gusau yayin wani taron masu ruwa da tsaki da ƙungiyarsa ta masu goyon bayan siyasar sa wato ƙungiyar siyasa ta Jajiyya ta shirya.
A cewar sa, akwai buƙatar gwamnatin jihar ta tallafa wa ‘yan jam’iyya domin su shiga kowane lungu da saƙo na jihar don neman goyon baya ga jam’iyyar a yanayin siyasa da ake ciki a yanzu.
Ya jaddada buƙatar ɗaukar ‘yan jam’iyyar daga dukkan ɓangarorin jam’iyyar a jihar a matsayin abu guda, yana mai cewa haɗin kai yana da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da nasara ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Dauda Lawal a zaɓe mai zuwa.
“Ya kamata a jawo ‘yanyan jam’iyyar daga ɓangarori daban-daban don cimma nasara a yaƙin neman zaɓe Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Dauda Lawal kuma kada a bar su a gefe,” in ji shi.
Hon. Jaji ya nuna cewa haɗin kai tsakanin ‘yanyan jam’iyya ya kasance mafi kyawun zaɓi ga APC a Jihar Zamfara a wannan lokacin.
Ya jaddada cewa ya zama dole ga shugabannin jam’iyyar a jihar su ɗauki dukkan ‘yan jam’iyya a matsayin abu ɗaya ba tare da nuna wariya ba.
“Na san ƙalubalen da ake fuskanta tsakanin ‘yanyan jam’iyyar APC a Jihar Zamfara, kuma za mu tabbatar da cewa kowace ƙungiya ta sami kulawar da ta dace don cimma nasarar da ake so,” in ji Jaji.
Ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar APC a jihar da su ci gaba da bin doka da oda tare da haɗin kai domin tabbatar da nasara ga Shugaba Tinubu, Gwamna Dauda Lawal da dukkan ‘yan takarar APC a zaɓe mai zuwa.
