Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya ƙaddamar da motocin sufuri 30 CNG masu amfani da dizal da wutar lantarki, tare da keke Napep na lantarki 200 a Jihar Katsina.
Motocin za su yi aiki a Katsina, Daura da Funtua, yayin da jihar ke shirin samar da tashoshin sufuri na zamani guda 40 domin sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a.
Shirin keke napep ɗin na daga cikin shirin jihar na samar da keke 500, wanda ake sa ran zai ƙirƙiri damammaki ga matasa da masu sana’ar sufuri.
Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa ya bayyana shirin da cewa “Daga sauyin makamashi zuwa sauyin tattalin arziki”, yana mai cewa manufarsa ita ce inganta sufuri, samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arzikin Katsina.
Haka kuma duk a ziyarar aiki na yini guda mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya ƙaddamar da manyan tagwayen hanyoyi a cikin birnin Katsina.
