
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shirya barin Legas zuwa Abuja a yammacin ranar Litinin bayan shafe kwanaki shida a tsohuwar babbar birnin tarayyar.
A ranar 29 ga Satumba ne Tinubu ya isa Legas bayan kammala hutunsa na shekara a Landon da Paris. Yayin zamansa a Legas, Shugaban ya gabatar wa ‘yan Nijeriya jawabi a ranar 1 ga Oktoba, wato lokacin bikin cikar Nijeriya shekeru 66 da samun ‘yancin kai.
Bayan haka a ranar, Shugaban ya kuma halarci taron karrama marigayi MKO Abiola musamman akan gwagwarmayarsa ta siyasa da kuma tarihin “June 12” bayan gwagwarmayar dawo da mulkin dimukraɗiyya a Nijeriya.
Haka kuma, shugaban ya kai wa Oba na Legas, Oba Rilwan Babatunde Akiolu ziyara a ranar Lahadi a fadarsa ta Idu Iduganran da ke Lagos Island.
Ziyarar ta Legas ta zo ƙarshe ne Yayin da aka tsara cewa Shugaban zai koma Abuja a wannan yammacin, kamar yadda Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya bayyana a wata takarda.
