Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ɗage hukuncin neman belin El-Rufa’i

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Litinin, 5 ga Oktoba, Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zaune a Kaduna ta ɗage zaman sauraron ƙorafin da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i ya shigar mata na ƙalubalantar hukuncin Babbar Kotun Jihar Kaduna da ya yi watsi da buƙatarsa ta neman beli.

El-Rufa’i, wanda Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta gurfanar da shi, ya tunkari Kotun Ɗaukaka Ƙarar ne domin neman ta soke hukuncin Babbar Kotun da bayar da belin nasa daga kotun ta ƙi amincewa da shi.

Da yake ganawa da ‘yan jarida jim-kaɗan bayan zaman, lauyan da ke kare ɓangaren ICPC Ayodeleji Adelukpe, ya ce tsohon gwamnan ya je gaban kotun ne da ƙorafin ƙalubalantar hukuncin da Babbar Kotun ta yanke akan neman belinsa, inda sau uku Babbar Kotun tana watsi da buƙatar bisa la’akari da rashin cika wasu sharuɗɗa, ciki har da rashin nuna wani iyakancewa a kai.

Ya bayyana cewa, suna ƙalubalantar ɗaukaka ƙarar ne saboda alƙalin da ya yi watsi da na baya ya yi abin yake she ne daidai saboda an gaza bayyana dalilin da ya sa suke ganin ya dace a amince wa ƙorafi na biyun duk da cewa ba su nuna wani iyakancewa ba, sannan ba a sanar da kotun shigar da na ukun ba.

Saidai a nasa ɓangaren, lauya mai kare wanda ake ƙara, Paul Erokoro (SAN) ya bayyana ƙwarin-gwiwar cewa Kotun Ɗaukaka Ƙarar za ta amince da buƙatar tasu ta bayar da belin tare da soke hukuncin babbar kotun bisa ƙorafin nasu. Erokoro ya bayyana kama El-Rufa’i a matsayin abin da aka siyasantar, yana mai cewa tsohon gwamnan bai aikata laifin cin amanar ƙasa ko halaka wani ba kuma abin da aka maka shi akansu na bayar da beli ne.

By Babaji

Leave a Reply