Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Zallawa na da ƙungiyoyinsu da ajandarsu tun kafin shigowar soshiyal midiya kuma akasari ƙungiyoyin addinin Kirista ne da ke ƙorafin a na son Musuluntar da Arewa ƙarfi da yaji.
Wallahi ina sauraron wani shirin rediyo a Abuja sai na ji a na hira da wani malamin coci daga jihar Filato da ke cewa wai ɓarayin daji na karisa aikin da su Shehu Mujaddadi ne su ka yi. Wannan ba sabon abu ba ne in an duba wasiƙar da wasu su ka aika Amurka su na cewa akwai ajandar Shehu ta isar da Musulunci har tekun Atalantika. Paston nan da ke iƙirarin ya na da jinin Fulani da Barebari duk da ƙabilar Midibelawa ne, ya zayyana bayanai filla-filla tamkar yadda Zallawa ke surutan nan na kwangila da mafi akasari ta amfani da sunayen bogi.
Baya ga ƙungiyar HAUSA CHRISTIAN DEɓELOPMENT INITIATIɓE da ta jagoranci naɗa Rabaran Shu’aibu Bargi a matsayin Sarkin Hausa Kiristoci na Kano da taken BAHAUSA YA MULKI KANSA akwai ƙungiyoyi da ke amfani da sunan Hausa da sun sha fitowa ƙarara su na kokawa cewa a na nunawa Hausawa Kirista wariya. ɗaya daga ƙungiyoyin HACFO tun 2018 ta fitar da sanarwa wacce da na karanta sai na ga kwabo da kwabo shi ne aikin da Zallawa ke yi a yau.
Ga 7 daga ƙorafin wasu ƙungiyoyin mabiya da ƙungiyar HACFO ta kirista bayan wahayi da ubangiji ya yi wa shugaban ƙungiyar a ranar 28 ga watan Yuli 2017:
1. Nuna wariya ga mabiya addinin Kirista a Arewa musamman Hausawa.
2. Kore samuwar Hausawa
3. Neman Musuluntar da Arewa ƙarfi da yaji
4. Ayyukan Shehu Mujaddadi ne a yanzu ɓarayin daji ke karisawa
5. Fasiƙanci da ‘yan mata mabiya addinin Kirista
6. ɗauke Kiristoci ko sace su.
7. Tilasta mata Kiristoci auren dole tun su na ƙanana.
Duk mai hankali ya ga daga inda ajandar Zallawa ta samo tushe gabanin ‘yan AIFOB da ‘yan siyasa su kutso cikin lamarin don biyan muradunsu na ɗarewa madafun iko da yiwuwar cin amanar ƙasa.
Ba ƙungiya ko ɗaya ta Hausawa Musulmi a duk duniya domin addini ba ruwansa da wata ƙabila indai addinin na Allah ne. Hatta wadannan ƙungiyoyin mabiya na Arewa na yin ra’ayinsu ne kawai amma ba su da hujja ta sisin kobo a Baibul kama daga Littafin FARAWA a tsohon alƙawari GENESIS zuwa AYYUKAN MANZANNI a sabon alƙawari REɓELATION. Ko Musulmi a tsakanin Igbo da ke ayyana kansu a matsayin IGBO MUSLIMS na yin haka ne wataƙila don a na ganin abun mamaki ne a samu Igbo Musulmi kuma akasarin kafafen yanar gizo na ‘yan kudu maso gabar na watsi da duk wani “Igbo muslim” don sun ce hakan neman shigar mu su ta’addanci ne yankinsu kuma sam ba za su lamunta ba.
A na batun wasu ƙungiyoyin mabiya addinin Kirista da ke korafin za a musuluntar da arewa; zallawa na jero wasu Fulani mabiya addinin Kirista. Muradun ƙungiyoyin na masihiyya, kwabo da kwabo su ne ƙururuwar da zallawa ke yi yau a soshiyal midiya
Kamar fa mutum ne ya ce Isra’ila na kai wa Falasɗinawa hari, sai wani ya yi caraf ya ce ai Hezbollah ma na kai wa Isra’ila hari. Son zuciyar a nan da shashantar da magana shi ne maimakon a duba kadun Falasɗinawa sai a koma a na ai ga wasu can ma na tsokana. A a in an ce Amurka ta kai hari Siriya sai wani ya ce ai Rasha ma ta shigo ta ɗauke tsohon shugaba Bashar Al’Asad.
Mun kawo fa rubutattun hujjoji daga wasu ƙungiyoyin mabiya addinin kirista da Fastoci da ke alaƙanta kansu da Hausawa na yadda su ke zargin Musulmi na neman Musuluntar da Arewa ƙarfi da yaji da kuma tauye haƙƙin mabiya addinin Kirista Hausawa, zagin Shehu Mujaddadi da ƙarara alaƙanta shi da ɓarayin daji na zamanin yau. Juya tajdidin Mujaddadi zuwa mugun abu har ma da wai muradunsa ‘yan ta’addan daji ke karisawa na neman kai Musulunci har tsakiyar tekun Atalantika.
Waɗannan maganganu su ne kwabo da kwabo ayyukan da a yau wasu Gwarawa da ke iƙirarin “Bahaushe ya mulki kansa” ke rurutawa a shafukan soshiyal midiya. Shin ko waye Bafulatani a wajen su? AMSA shi ne Musulmi Bahaushe! In an kara matsawa gaba shi ne wanda ya haɗa kai da Bafulatani ya ke watsi da shirka da ayyukan bori na zamanin jahiliyya da ƙin bin koyarwar Bature ta maida zaman duniya hayaƙin taɓa don haka a more rayuwa, katti su saka gajeren wando mata su saka gashin doki! Hausawa sun ce dole a bi umurnin Allah matuƙar a na son rabauta a gobe kiyama. Wannan ya sa Bature ya kwashi rabonsa a wasu sassan Arewa na waɗanda su ka karɓi addininsa na masihiyya inda mafi rinjaye su ka cigaba da ɗorawa kan tarbiyyar da Shehu ya shimfiɗa ta TAUHIDI TSANTSA ba tsunbure ba sakarci ba raba kafa ba kame-make ba camfe-camfe ba Giji ba giza-gizai ba ɗakin Doguwa ba Tsunburbura ba Barbushe balle Gijimasu.
Zallawa sun zama sojojin soshiyal midiya na wancan aiki na wasu ƙungiyoyin masihiyya masu alaƙanta kansu da Hausa don haka su ka yi shigar burtu ta hanyar ƙirƙiro shafukan karya da sunayen karya da mannewa musulunci don haddasa fitina tsakanin Hausawa da Fulani a yi ta dauki ba daɗi tsakanin Musulmi don cimmawa Midibelawa da AIFOB muradunsu na aware. Yanzu kuma wasu ‘yan siyasa sun shigo don neman madafun iko ta barauniyar hanya da kuma rage ƙarfin tasirin Arewa a dandalin dimokraɗiyyar Nijeriya.
TAMBAYA-shin a ina ƙungiyoyin da su ke kawowa na Fulani Kirista su ka koka kan musulmi na neman Musuluntar da Arewa ƙarfi da yaji ko kuma a ina su ke zagin musulmi ko a ina su ka nada sarakunan Fulani mabiya addinin Kirista na Kano ko Katsina ko ma garuruwa irin Zangon Kataf? Kai a wadanne shafuka su ke ɓoye kansu su na fesa dafin maciji na ruruta fitinar ƙabilanci?
Kowa na da hurumin yin addininsa amma kowa ba shi da hurumin fakewa da addini don zagin wani addini.
Da zarar an yi magana kan su sarkin mabiya addinin Kirista na kano Rabaran bargi, sai zallawa su wurgo hoton Rabaran Buba na fulcan! Maratani; a na maganar addini, su zallawa na jefo ƙabila don shi ne jigon kwangialrsu ta haddasa yaki a arewa wanda kuma idan an kyale har wannan akasi ya faru, to gaskiyar magana ‘yan ƙalilan ne za su tsira don haka ya ke da muhimmanci a yi tsayin daka wajen watsawa zafin fitinar rowan sanyi.
Ba ma yanzu da na ke jerin rubutun nan kan kungiyoyin kirista masu alaƙanta kansu da Hausawa da manufofinsu ne sammakal Zallawa ke ɗabbakawa ba; duk lokacin da na kawo batun Maguzawa ko naɗin Sarkin Hausawa Kirista na Kano Rabaran Shu’aibu Bargi, sai Zallawa su wurgo hoton shugaban ƙungiyar Fulani mabiya masihiyya Rabaran Buba Aliyu. Dabararsu a nan ita ce tun da sun yi karyar su Hausawa ne alhali asalin Gwarawa ne kuma masu bin rayuwar Yammawa; sai su karkatar da darasin zuwa ai su ma Fulani su na da mabiya addinin Kirista har da ƙungiya ƙarƙashin jagorancin Rabaran Buba Aliyu.
Duk duniya ba ƙungiyar Hausawa musulmi kuma ba ƙungiyar Fulani Musulmi – mai ya sa? AMSA- Don dalilai biyu:
1. Musulunci addinin Allah ne kowa da ke Musulmi na amsa KALMAR SHAHADA ne ba ƙabila ba. Ware wani don ƙabilarsa haramun ne a Musulunci.
2. Hausawa da Fulani ba sa buƙatar su ayyana kan su a matsayin Musulmi don da ka ji sunansu ka na maganar musulunci ne. Haƙiƙa akwai waɗanda ba Musulmi a cikinsu amma su ne marar sa rinjaye.
Na kawo mu ku labarin faifan bidiyo inda Farfesa Daniel Danladi Musa na jami’ar tarayya ta Dutsinma ke jagorantar naɗa Reɓerend Bargi ya na mai nuna ai wai an ce Bahaushe ba zai mulki kansa ba, to ga shi an samu Sarki Bahaushe kuma Kirista a Kano. Wannan ya nuna adawa da sarakunan Arewa ba don alaƙarsu ta tarihi da Fulani ba ne, a’a, don su Musulmi ne!. Shin wannan shi ne BAHAUSHE YA MULKI KANSA?.
Masu wurgo hotunan Rabaran Buba ba su kawo inda ya naɗa Sarkin Fulani Kirista a Filato inda ya ke da zama ko ya shiga Zangon Kataf ko Makurdi ba, balle ya shiga Anacha ko Enugu don nada sarautar a tsakanin ‘yan ta’addan ESN ba. Rabaran Buba mai tushen zama a Jos jihar Filato, na cikin majami’ar EYN ne kuma memba ne a majalisar Fada-Fada/BISHOPS na ɗarikar Katolika na Nijeriya. Ya sha kokawa kan yadda Zallawa ke yi tattara dukkan Fulani su manna mu su ta’addanci, alhali ya ce ga su nan su Kirista ne. Kiristancin Buba bai tserar da shi daga kuɗin goron su Rabarn Ezekiel Dachomo, Wilfred Chikpa Anagbe, Aleɗ Birbir da Zallawa ba. Wannan ya nuna Zallawa na da ajandar cimmawa ƙabilu Midibelawa da AIFOB burinsu na aware. Da yawa sun fi fahimtar a ce ‘yan Biyafara ne ke son ballewa daga Nijeriya. A nan karin haske shi ne wadanda su ka ƙirƙiri yanki mai suna MIDIL BEL a Arewa ta tsakiya na da burin ware kansu daga kokuwar Arewa don sun ki jinin a dangantasu da Arewa.
KAMMALAWA
Kamar yadda Kiristancin Rabaran Buba bai amintar da shi daga zunduma ashar na Zallawa ba, hakanan duk wani dan karamar ƙabilar Zallawa a Arewa ba zai samu karɓuwa a wajen ‘yan Biyafara ba, matukar ashanar da su ke kyastawa Arewa ta kama da wuta. Midibelawa da ke ɗaukar kan su kirista na ganin Rabaran Buba Aliyu na FULCAN a matsayin wani waƙe-wae inda su ɗin ma haka AIFOB za ta ɗauke su kura-kura!
