NAHCON ta karɓi baƙuncin Babban Kwamandan Sibil Difens don ƙarfafa alaƙar aiki

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Laraba, 7 ga Oktoba, 2026 Babban Kwamandan Hukumar Tsaron Fararen Hula ra Ƙasa (NSCDC) da aka sani da Sibil Difens, Dakta Ahmed Abubakar Audi, ya kai ziyarar girmamawa ga Shugaban Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON), Ambasada Isma’il Abba Yusuf a ofishinsa da ke hedikwatar hukumar ta Hajj House a Abuja.

Wannan ziyara ta taimaka wajen samar da damar tattauna muhimman al’amuran da suka shafi ƙarfafa alaƙar aiki tsakanin NAHCON da NSCDC musamman a lamuran da suka shafi tsaro, gudanar da dandazon jama’a da amincin alhazai da kuma samar da ingantaccen yanayi na haɗin-gwiwa yayin gudanar da harkokin hajji.

A wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran NAHCON, Shafi’i Sani Mohammed ya fitar, ya ce kwamandan na NSCDC ya yaba wa jagorancin Ambasada Yusuf da kuma gyare-gyaren da ake yi a NAHCON a ƙarƙashin ikonsa musamman da nufin daidaita al’amuran masana’antar hajjin Nijeriya akan ingantaccen tsari, yana mai alƙawarin samun goyon baya da haɗin kan NSCDC domin ciyar da harkokin hukumar gaba.

A nasa jawabin, Ambasada Isma’il Yusuf ya jinina wa kwamandan bisa wannan ziyara, inda ya jaddada masa ƙoƙarin hukumar ta ƙarfafa alaƙa tsakanin hukumomin biyu don maslahar alhazai da samun nasara yayin aiwatar da harkokin hajji.

By Babaji

Leave a Reply