Shugaban ƙaramar hukumar Talata Mafara ya caccaki shugaban APC na Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Shugaban ƙaramar hukumar Talata Mafara, Hon. Yahaya Yari, ya yi Allah wadai da kalaman da ake dangantawa ga shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na Jihar Zamfara, Alh. Kabiru Moyi Birnin Magaji, wanda ya yi zargin cewa Gwamna Dauda Lawal baya tallafawa ‘yan jam’iyya.

An ruwaito cewa Alh. Kabiru Moyi ya yi wannan zargin ne a lokacin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar da ke Gusau kwanaki kaɗan da suka gabata.

Da yake mayar da martani kan lamarin a ranar Laraba, Hon. Yahaya Yari ya bayyana kalaman a matsayin ƙarya, rashin ladabi da kuma cin mutuncin gwamna.

Ya ce abin takaici ne yadda shugaban jam’iyya na jiha zai faɗi irin wannan magana duk da cewa shi ne wanda ya fi cin gajiyar gwamnatin Gwamna Lawal kai tsaye.

Hon. Yari ya bayyana cewa an ba shugaban jam’iyyar APC kwangilar da ta kai Naira Miliyan N87m a ƙarƙashin gwamnatin yanzu, amma ya kasa tallafawa jama’a a matakin ƙasa.

“An ba Shugaban jam’iyyar APC, Hon. Kabiru Moyi Birnin Magaji, kwangilar Naira Miliyan 87. Mutum nawa ya saya wa mashin a garinsa? Mutum nawa ya tallafawa da jari don fara kasuwanci?” In ji Hon. Yari.

Ya ce kalaman shugaban jam’iyyar na iya haifar da rarrabuwar kai a cikin jam’iyya tare da ɓata sunan gwamnatin da ta ke ɗaukar kowa a jiki.

A cewarsa, mambobi masu kishin jam’iyya ba za su sake zura ido suna kallon wasu na ɓata sunan Gwamna Dauda Lawal ba.

“Muna tare da Gwamna Dauda Lawal ɗari bisa ɗari. Daga yanzu ba za mu lamunci duk wani mutum ko gungun mutanen da suka ci mutuncin gwamna ba. Dole ne a daina irin wannan rashin kunya,” in ji shi.

Hon. Yari ya gargaɗi shugaban jam’iyyar APC da ya daina yaɗa maganganu marasa tushe a kan Gwamnan ko kuma su ɗauki mataki a kansa.

Ya kuma sake jaddada cikakken biyayya da goyon bayan al’ummar ƙaramar hukumar Talata Mafara ga Gwamna Dauda Lawal da ajandar ceton Jihar Zamfara.

By ukarofi

Leave a Reply