Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Safiyar Alhamis ɗin nan ne waɗansu shafukan sada zumunta suka karaɗe yankin Argungu da ke jihar Kebbi inda su ke ta wallafa maganganu daban-daban da ke cin karo da juna suna nuna ‘yan bindiga sun kai hari tare da mamaye babban kamfanin shinkafa na WACOT da ke kan hanyar Sokoto.
Wakilin Jaridar Blueprint a Kebbi ya kai ziyarar gani da ido inda ya zanta da waɗansu mutane a wajen duk da ya ke dai an kulle ƙofofin kamfanin tare da ɗaukar matakan ko-ta-kwana kuma mutanen da ke wajen duk sun gudu sai dai jami’an tsaro da aka girke a wajen.
Wani matashi Ibrahim Garba ya bayyana cewa sun sami labarin lakurawa na kan hanyar Sokoto zuwa Argungu ne a ƙauyen Wali sai dai babu tabbacin yadda abin ya ke.
Malam Adamu Lawal wani mazauni ƙauyen Fakon Sarki ya bayyana cewa ba wani abu mai kama da wannan kuma kamar yadda ka ke gani ga motoci nan suna kai-komo ba wata alamar tashin hankali.
Sai dai ya ji an ce manoma ne su ka ga ayarin waɗannan ‘yan bindiga ne yayin da su ke wucewa su kuma suka tsorata suka gudu zuwa cikin gari suna cewa ga lakurawa nan zuwa.
Malam Abubakar Bayawa da ke ƙaramar hukumar Augie ya bayyanawa wakilin Jaridar Blueprint Manhaja ta wayar tarho da cewa lallai an ga ayarin waɗannan ‘yan bindiga suna wucewa ta gefen Bayawa duk da ba su taɓa kowa ba amma dai mutane musamman mata sun firgita inda suka fito aguje daga cikin gidajen su suna kara-kaina cikin gari amma dai maganar gaskiya ba wani tashin hankali sun dai wuce ne kan baburan su ba tare da sun taɓa kowa ba.
Shugaban karamar hukumar Argungu Honarabul Aliyu Sani Gulma tare da ɗan majalisar dokoki ta jihar Kebbi mai wakiltar karamar hukumar Argungu Honarabul Umar Na-amore sun isah garin na Wali domin gani da ido game da abinda ake yadawa inda mutanen garin suka shaida musu da ba wata matsala.
Shugaban ƙaramar hukumar Argungu ya yi kira ga al’umma musamman masu amfani da kafafen sada zumunta na zamani da su ji tsoron Allah su daina yaɗa labarun ƙarya.
Yanzu haka dai an girke jami’an tsaro a kan wannan hanyar yayin da waɗansu kuma su ke sintiri.
A ɗaya bangaren kuma bayanai daga yankin karamar hukumar Arewa da Bagudo sun nuna yanzu haka dai ‘yan bindiga da a ke sa ran mayaƙan lakurawa ne suna cin karen su ba babbaka inda yanzu haka su ke riƙe da ikon waɗansu ƙauyuka.
Waɗansu bayanai kuma a baya-bayan nan sun bayyana cewa an yi wa mayaƙan lakurawa kisan ƙare dangi a Shanga inda aka ce an hallaka sama da 50 safiyar ranar Laraba da ta gabata.
