Sauyin Sheƙa: Dan Majalisar Tarayya na Kura ya karɓi ƙungiyoyin APC zuwa NDC

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kura, Madobi da Garun Malam, Hon. Yusuf Umar Datti Kura, ya karɓi ƙungiyoyi sama da goma na jam’iyyar APC da suka sauya sheƙa zuwa NDC a yankin Kura.

An gudanar da taron ne a ranar Asabar da ta gabata a filin makarantar firamare da ke garin Karfi.

Da yake jawabi, Datti Kura ya ce sauyin sheƙar na nuna cewa al’umma sun fahimci, a cewarsa, irin matsin rayuwar da gwamnatin APC ta jefa ƙasar a ciki. Ya kuma yaba wa waɗanda suka shigo NDC, tare da cewa za su taka muhimmiyar rawa wajen faɗaɗa jam’iyyar.

Ya yi kira ga matasa da sauran al’umma da su tabbatar sun gyara katin zaɓensu, sannan su yi amfani da ƙuri’unsu a zaɓe domin neman sauyi.

A nasa jawabin, ɗaya daga cikin jagororin NDC a yankin, Alhaji Ado Ashafalalah, ya yi kira ga matasa da su guji duk wani abu da zai haifar da tashin hankali, yana kuma fatan samun nasarar jam’iyyar a zaɓukan shekara mai zuwa.

Shi ma Shugaban NDC na yankin Karfi, Ahmad Usman, ya bayyana taron a matsayin tarihi, yana mai cewa dimbin matasa maza da mata daga ƙungiyoyi daban-daban sun shiga jam’iyyar.

Wasu daga cikin waɗanda suka sauya sheƙar sun ce sun shiga NDC ne saboda gamsuwarsu da ayyukan ci gaba da Datti Kura ke gudanarwa a yankunan da yake wakilta. Sun kuma yi alƙawarin ƙara wayar da kan sauran magoya bayan APC domin su ma su shiga NDC.

ƙungiyoyin da suka sauya sheƙar sun haɗa da Sabuwar Karfi, Tafiyar Gidan Hon. Datti Kura, Karfi Political Moralist, Karfi Youth Progressiɓe Moɓement, Yakasai Depot NDC, da Ƙungiyar Masu Buƙata Ta Musamman, da dai sauransu.

By ukarofi

Leave a Reply