Muna zaune lafiya tare da sauran ƙabilun jihar Legas — Sarkin Hausawan Ladiboye

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

Sarkin Hausawan Unguwar Ladiboye da ke ƙaramar Hukumar Ikorodu Central a Jihar Legas, Alhaji Adamu Haladu Mohammed, ya bayyana cewa Hausawa mazauna yankin na ƙara samun zaman lafiya da kyakkyawar fahimta tare da sauran ƙabilun da ke zaune a yankin.

Alhaji Adamu, wanda kuma ɗan kasuwa ne kuma shugaban Kasuwar Ladiboye da ke Ikorodu, ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da wasu wakilan kafafen yaɗa labarai kan yadda zaman takewar al’ummar Hausawa da sauran ƙabilun da ke zaune a Unguwar Ladiboye da Ƙaramar Hukumar Ikorodu ke gudana.

Sarkin ya bayyana jin daɗinsa kan yadda kyakkyawar dangantaka da zaman lafiya ke ci gaba da wanzuwa tsakanin Hausawa da sauran al’ummomin yankin.

Ya ce tun bayan kafuwar Kasuwar Ladiboye zuwa yanzu, Hausawa da sauran ƙabilun da ke zaune a yankin suna gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali, ba tare da samun manyan matsalolin da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya a tsakaninsu ba.

Ya ƙara da cewa, wannan zaman lafiya na daga cikin abubuwan da suka taimaka wajen bunƙasar kasuwar, tare da inganta harkokin kasuwanci da ƙara yawan ’yan kasuwa da masu ziyartar yankin.

A cewarsa, daga cikin manyan abubuwan da kasuwar ta samu a cikin ’yan shekarun nan akwai ingantaccen zaman lafiya, ƙara samun tsaro da kuma ƙaruwa a yawan ’yan kasuwa daga sassa daban-daban.

Ya ce wannan ne ma ya sa yake ƙara jan hankalin Hausawa da sauran ƙabilun da ke zaune a Legas, musamman masu sha’awar gudanar da harkokin kasuwanci iri daban-daban, da su ziyarci yankin Ikorodu domin ganin yadda harkokin kasuwanci ke gudana a Kasuwar Ladiboye.

Sai dai Sarkin Hausawan ya bayyana cewa, duk da ci gaban da ake samu, ’yan kasuwa na fuskantar wasu ƙalubale, musamman hauhawar farashin man fetur, wanda ya ce yana yin tasiri kai tsaye kan harkokin kasuwanci da kuma rayuwar al’umma baki ɗaya.

Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ƙara himma wajen nemo hanyoyin rage wa talakawa raɗaɗin tsadar rayuwa, tare da ɗaukar matakan da za su taimaka wajen sauƙaƙa harkokin kasuwanci.

A wani ɓangare na jawabin nasa, Alhaji Adamu ya taya Nijeriya da ’yan ƙasar murnar cika shekaru 66 da samun ’yancin kai, tare da yi wa ƙasar fatan samun ci gaba da zaman lafiya mai ɗorewa.

Ya kuma yi kira ga matasan Arewacin Nijeriya, musamman yayin da zaɓe ke ƙara kusantowa, da su guji shiga harkokin bangar siyasa da ka iya jefa su cikin matsala ko lalata mutuncinsu.

Ya shawarci matasan da su mayar da hankali wajen neman ilimi, koyon sana’o’in dogaro da kai da kuma yin amfani da damarmakin da za su taimaka wajen inganta rayuwarsu da makomarsu.

By ukarofi

Leave a Reply