Hisbah ta yi garambawul ga jami’anta a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina a ƙarƙashin sabon shugabancinta, ta fitar da sabbin umarni da suka shafi amfani da muƙaman aiki, tantance jami’anta da kuma hana yaɗa bayanan sirri na hukumar a kafofin sadarwa ba tare da izini ba.

A cikin wata takardar sanarwa wanda darakta mulki na hukumar Malam Bello Gatari Barau ya aika wa kwamandojin hisbah na ƙananan hukumomi 34 na jihar, Hukumar ta buƙaci a tabbatar da bin ƙa’idojin aiki tare da ɗaukar matakan ladabtarwa kan duk wanda ya saɓa.

Sanarwar ta bayyana cewa an haramta wa jami’an hisbah ɗaukar, amfani da ko nuna wani matsayi da hukumar ba ta amince da shi a hukumance ba.

Haka kuma, an umarci kwamandojin ƙananan hukumomi su tabbatar da cewa kowane jami’i yana amfani da matsayinsa da sunan aikinsa da aka amince da su kawai.

Haka kuma hukumar ta hana jami’anta, musamman ma’aikatan sashen fasahar sadarwa (ICT), wallafa hotuna, bidiyo, tsokaci ko wasu bayanai ba tare da izini, musamman waɗanda suka shafi sirri, ayyuka da muhimman bayanan hukumar.

Sanarwar ta jaddada cewa duk wani bayani na hukuma da aka shirya fitarwa ga jama’a dole ne ya samu izini daga babban kwamanda na hukumar kafin wallafa shi.

Sanarwar ta buƙaci dukkan kwamandojin Hisbah su ɗauki umarnin da matuƙar muhimmanci tare da tabbatar da cikakken bin ƙa’idojin da aka shimfiɗa.

Matakin dai na zuwa ne a wani yunƙuri na ƙarfafa bin tsarin shugabanci, tabbatar da ingantaccen amfani da muƙaman aiki da kuma kiyaye bayanan hukumar daga yaɗuwa ba tare da izini ba.

By ukarofi

Leave a Reply