
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka (DHS) ta wallafa sunaye da hotunan ‘yan Nijeriya guda 24 da jami’an hukumar shige da fice suka kama su bisa zargin su da hannu a manyan laifuka yayin da gwamnatin Shugaba Donald Trump ta faɗaɗa ayyukan tabbatar da kiyaye dokokin shige da ficen ƙasar.
A cewar wata sanarwa da ma’aikatar ta wallafa a ranar Alhamis, jami’an Shige da Fice da Kwastom (ICE) na Amurka ne suka kama ‘yan Nijeriyar a wurare mabambanta a sassan ƙasar. Laifukan da ake zargin nasu da hannu aciki sun haɗa da damfarar waya, damfarar manhajar saƙo ta mel, satar kuɗi, ta’amali da ƙwayoyi, satar zama ɗan ƙasa, cin zarafi, amfani da bayanan bogi, karya dokar makamai da cin zarafin ƙananan yara.
DHS ta bayyana cewa, wannan ya nuna matakin rahotannin aikata munanan laifukan daga waɗanda ba amurkawa ba da jami’an tsaro suka cika hannu da su, tana mai cewa hakan wani ɓangare ne na cika alƙawarin Shugaba Trump da aiwatar da gagarumar kora ga ‘yan ƙasashen waje. Saidai, bayanan da DHS ɗin ta fitar ba su nuna ainihin matsayin kowane ɗaya daga cikin mutanen da ta fitar da bayanan nasu ba akan zaman ƙasar ko bayar da ba’asi kan matakin korar su daga ƙasar.
Ge jerin sunayen mutanen kamar yadda DHS ta fitar:
- “Emmanuel Omowaiye — Mail fraud; Richmond, Texas.
- Laurene Onwuka — Fraud and impersonation; Chantilly, Virginia.
- Olusegun Shonekan — Wire fraud; Newark, New Jersey.
- Olusegun Olaseni — Amphetamine sale; Greencastle, Indiana.
- Peter Ude — Wire fraud; Atlanta, Georgia.
- Newton Jemide — Wire fraud, conspiracy and mail fraud; Fort Dix, New Jersey.
- Shedrack Umukoro — Money laundering; Yazoo City, Mississippi.
- Olasoji Akinbode — Fraud and impersonation; Kearny, New Jersey.
- Oluwatosin Afolabi — Fraud; Conroe, Texas.
- Alameen Adetunji Tokosi — Drug possession; Chicago, Illinois.
- Joshua Ipoade — Wire fraud; Atlanta, Georgia.
- Michael Orji — Weapons violation, fraud, identity theft, wire fraud, false citizenship and money laundering; Oxford, Wisconsin.
- Ahmadu Apooyin — Drug-related offence; Baltimore, Maryland.
- Teslim Kiriji — Money laundering; Yazoo City, Mississippi.
- Onomen Uduebor — Identity theft; Seattle, Washington.
- Charles Ochi — Money laundering; White Deer, Pennsylvania.
- Daniel Eta — Wire fraud; White Deer, Pennsylvania.
- Ifeanyi Ibennah — Cruelty towards a child; Tampa, Florida.
- Kazeem Runsewe — Wire fraud; Thomson, Illinois.
- Fatiu Lawal — Wire fraud; Lompoc, California.
- Justin Akubueze — Money laundering; Orem, Utah.
- Moyinoluwaseun Okeowo — Larceny, forgery and concealing stolen property; Orlando, Florida.
- Babajide Oluwaseun Faseyi — Assault; Alden, New York.
- Bright Eigbedion — Money laundering; Lompoc, California.”
