Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Makarantar Madarasatul Da’awunul Umma Litahagizul ƙur’an da ke cikin ƙaramar Hukumar Bichi ta gudanar da bikin saukar karatun Alƙur’ani mai girma na ɗalibai 89 a ranar Lahadi a harabar makarantar.
Bikin ya samu halartar manyan malamai, limamai da ’yan siyasa, ciki har da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda Mataimakinsa, Alhaji Murtala Sule Garo, ya wakilta.
Da yake jawabi a wajen bikin, Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo, ya bayyana muhimmancin karatun Alƙur’ani a cikin al’umma.
Ya ce wannan ba ƙaramin abin alheri ba ne ganin yadda yara suka sauke wannan littafi mai daraja, tare da yabawa malaman makarantar da iyayen yaran bisa jajircewar da suka yi wajen tabbatar da cewa yaran sun samu wannan babban alheri.
Kazalika, Mataimakin Gwamnan ya bayyana godiyarsa ga waɗanda suke tallafawa ilimi a yankin, musamman ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar yankin Inginiya, Abba Abubakar Bichi, wanda, a cewarsa, tun kafin ya zama ɗan Majalisa yake taimaka wa al’ummar yankin wajen ci gaban ilimi.
Ya kuma yaba wa waɗanda suka assasa wannan makaranta, musamman iyalan marigayi Alhaji Sani Buji Bichi.
Ya ƙara da cewa Gwamnatin Jihar Kano a shirye take wajen tallafawa ilimin addini da makarantun Islamiyya a faɗin jihar domin ci gaban addinin Musulunci.
Ya ɗauki alkawarin kammala wasu ayyukan ajujuwa a makarantar tare da ƙarin ɗaukar malamai domin inganta harkar karatu a makarantar.
Ya kuma yi kira ga al’umma, musamman mawadata, da su yi koyi da irin halin marigayi Alhaji Sani Buji Bichi na assasa ayyukan alheri domin ci gaban al’umma ko bayan rasuwarsu.
Mataimakin Gwamnan ya kuma ba da tallafin kuɗi naira miliyan ɗaya ga malaman makarantar, tare da ba da naira dubu 20 ga kowane ɗalibi a madadin Gwamnatin Jihar Kano.
Ya taya ɗaliban murnar wannan saukar da suka yi, inda ya yi kira a gare su da su yi amfani da abin da Alƙur’ani ya koyar, ba iya karantawarsa kawai ba.
A nasu bayanin, Shugaban ƙaramar Hukumar Bichi, Alhaji Hamza Sule Maifata, da ɗan Majalisar Jihar Kano mai wakiltar yankin a Majalisar Dokokin Jihar Kano, Hon. Lawan Shehu, sun jinjinawa waɗanda suka kafa wannan makaranta, tare da nuna farin cikinsu da Allah ya nuna musu wannan rana.
Sun kuma ba da nasu tallafin ga ɗaliban da suka yi saukar da kuma malaman makarantar.
Da yake jawabi ga manema labarai a madadin iyalan marigayi Alhaji Sani Buji Bichi, Malam Lamido Akilu Bichi, ya bayyana godiyarsu ga mahalarta bikin, musamman Mataimakin Gwamnan da ya wakilci Gwamnan Jihar Kano.
Ya ce wannan rana ce mai ɗimbin tarihi wadda ba za su manta da ita ba.
Ya kuma yi fatan cewa a shekara mai zuwa yawan ɗaliban da za su yi saukar zai ninka na bana.
Shi ma da yake jawabin godiya, Shugaban Makarantar, Malam Muhammad Sani Abdurrashid, ya bayyana farin cikinsa ganin yadda gwamnati ta ɗauki nauyin kammala wasu ayyuka a makarantar, tare da tallafa wa ɗalibai da malaman makarantar.
Ya bayyana hakan a matsayin wata gagarumar nasara ga makarantar da kuma al’ummar yankin.
Dangane da fifikon da ake samu a mafi yawan makarantun Islamiyya yayin saukar Alƙur’ani, inda ake samun ɗalibai mata da yawa fiye da maza, malamin ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da sauran shugabanni da su tashi tsaye wajen magance wannan matsala.
Ya ce babban abin da ke haifar da hakan shi ne halin matsin rayuwa da ake ciki, inda a cewarsa, a yanzu samari sun fi mayar da hankali wajen neman abin da za su ci da kuma zuwa wuraren wasanni.
ɗaliban da suka yi saukar sun haɗa da ɗalibai mata 67, maza 20, tare da wasu biyu da suka haddace Alƙur’ani.
