Blueprint ta gargaɗi ma’aikatanta ga faɗa wa tarkon fasahar AI yayin da ta horar da su

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar gudanarwar Kamfanin jaridun Blueprint ta gargaɗi ma’aikatanta akan faɗa wa tarkon ayyukan fasahar AI (artificial intelligence), tana mai cewa dukkan ‘yan jaridar da suka gaza gano ayyukan bogi bayan sun karɓi horo, za a hukunta su muddin aka same su da aiki da ire-irensu a ayyukansu ta hanyoyin da ba a amince da su ba.

Daraktan harkokin editancin jaridar, Clem Oluwole ne ya bayar da wannan gargaɗi yayin taron bada horo na kwana biyu akan AI ga ingancin ayyuka da kare martabar editanci, wanda hukumar ta gudanar a Abuja.

Oluwole ya ce, wannan horo na da nufin kimtsa ‘yan jarida da ƙwarewa wajen bambance sahihan hotuna, bidiyoyi da wasu ayyuka da AI ta samar da ayyukan da aka jirkita kafin wallafawa.

Ya yi gargaɗin cewa, kamfanin ba zai sake lamuntar kurakuran da za a iya kauce musu ba yayin ayyuka waɗanda ka iya rage ingancin aiki, musamman bayan bai wa ma’aikata damar samun ƙwarewa akan muhimman ababen da aikin jarida yake buƙata.

Ya bayyana cewa, jaridar ta gaggauta gudanar da taron ne bayan ta wallafa wani hoto na Shugaba Bola Ahmed Tinubu da daga bisani aka gano cewa na fasahar AI ne, lamarin da ya sa ta ga dacewar ta ankarar tare da horar da jami’an nata akan yadda za su gudanar da ayyukansu bisa ƙwarewa.

A nasa jawabin, Shugaban Hukumar Gudanarwa da Walwalar Ma’aikatan Blueprint, Nuhu Sani, ya ce an shirya taron ne domin wayar da kan ma’aikata akan lamuran ci-gaban fasahar zamani da yadda yake da tasiri ga masana’antar yaɗa labarai.

A cewarsa, hukumar gudanarwar ta haɗa hannu da abokin hulɗa akan cigaba da ƙoƙarin wayar da kan waɗanda suka halarta don tabbatar da sun aiwatar da horon da suka samu a harkokinsu na yau da kullum bisa tsari. Ya kuma ce, za a cigaba da samar da shirye-shiryen da za su taimaka wa inganta lamuran ma’aikata a fannoni daban-daban a nan gaba.

By Babaji

Leave a Reply