Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya, NLC, reshen jihar Katsina, ta nuna goyon bayanta ga sabon tsarin fansho, tare da kira ga ma’aikata da su fahimci yadda tsarin yake aiki, maimakon shiga fargaba kan yadda za a aiwatar da shi.
Shugaban ƙungiyar NLC ta jihar Katsina, Kwamared Nasir Wada Mai’adua, ne ya bayyana hakan yayin wani taron wayar da kan ma’aikata da tattaunawa kan walwalarsu, wanda ofishin mai bai wa Gwamnan Jihar Katsina shawara kan ƙwadago da haɓaka ayyuka ya shirya, tare da haɗin gwiwar NLC da sauran ƙungiyoyin.
Kwamared Mai’adua ya ce an shirya taron ne domin ilmantar da ma’aikata kan sabon tsarin fansho, sauraron ƙorafe-ƙorafensu, da kuma tattauna hanyoyin inganta walwalarsu.
Ya bayyana cewa sabon tsarin na iya samar da ingantacciyar hanya wajen gudanar da harkokin fansho fiye da tsarin da ake amfani da shi a baya.
Da yake magana a madadin mai bai wa gwamnan shawara kan ƙwadago da haɓaka ayyuka, daraktan gudanarwa da samar da kayayyaki, Alhaji Abdullahi Muhammad Raɗɗa, ya ce ziyarar tattaunawar ta bai wa ma’aikata damar gabatar da ƙorafe-ƙorafensu da matsalolin da suke fuskanta, domin isar da su ga gwamnatin jihar.
Alhaji Raɗɗa ya jaddada aniyar gwamnatin jihar na ci gaba da kyakkyawar alaƙa da ƙungiyoyin ƙwadago, yana mai cewa ma’aikata na da muhimmiyar rawa wajen gudanar da mulki da samar da ayyukan da al’umma ke buƙata.
Ya bayyana biyan albashi a kan lokaci, biyan bashin fansho da kuma biyan sauran haƙƙoƙin ma’aikata a matsayin wasu daga cikin matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka domin inganta walwalar ma’aikata.
Alhaji Raɗɗa ya yaba wa NLC da sauran ƙungiyoyin ƙwadago bisa haɗin kan da suke bai wa gwamnati, yana mai cewa tattaunawa a kai a kai na da muhimmanci wajen magance matsalolin ma’aikata da tabbatar da zaman lafiya a wuraren aiki.
Taron ya ƙunshi zaman tambayoyi da amsoshi, inda ma’aikata suka gabatar da tambayoyi tare da tattauna batutuwan da suka shafi sabon tsarin fansho, ɗaukaka darajar aiki da sauran buƙatun walwalarsu.
