Dangote ya buɗe damar sayen hannun jarinsa ga jama’a, amma abin tambaya shi ne: shin mutanenmu na Arewa za su yi amfani da wannan dama?
Alhaji Aliko Dangote ɗan Arewa ne, Musulmi kuma Bahaushe. Yanzu ga wata dama ta zo har gida, amma wasu ’yan Arewa kamar ba su damu da ita ba.
A ranar 13 ko 14 ga watan Satumba ne aka buɗe wannan damar sayen hannun jarin, yayin da a gefe guda ake ganin mutane daga sauran yankunan ƙasar suna ta neman damar mallakar kaso a kamfanin. Mu kuma, wasu daga cikinmu sai suka mayar da lamarin da kalaman da ba su dace ba.
Allah Ya sa kada mu zo daga baya muna nadamar rashin amfani da wannan dama.
Dangote dai ba ɗan siyasa ba ne, balle a ce mutum ya ƙi sayen hannun jarinsa saboda bambancin jam’iyya ko ra’ayin siyasa. Idan ba ka da wata hujja ta zahiri da za ta hana ka shiga harkar, bai kamata siyasa ta zama dalilin ƙin amfani da damar zuba jari ba.
Mu dai fatarmu ita ce Allah Ya ƙarfafi Alhaji Aliko Dangote, Ya sa duk wanda yake da kyakkyawar niyya Ya hore masa, yayin da duk mai mummunar niyya Allah Ya kare al’amarin daga sharri.
Allah Ka sa mu shiga sa’a, Ka kuma ba mu ikon amfani da damar da za ta amfanar da mu da al’ummarmu.
Daga MUKHTAR IBRAHIM SAULAWA, KATSINA.07066434519/08080140820.
