
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Amurka ta sanya Nijeriya a jerin ƙasashen da suka saɓa wa Dokarta ta Haramta Ɗaukar Ƙananan Yara Aikin Soja (CSPA), tana mai gargaɗin hakan ka iya janyo ta sanya wa Nijeriya takunkumin horar da sojoji, siyar da makamai, ɗaukar nauyin sojojin waje da haɗin kai kan tsaro daga ranar 1 ga Oktoba, har sai an samu alfarmar Shugaba Donald Trump.
Wannan al’amari ya biyo bayan rahoton 2026 da Ma’aikatar Kula da Lamuran Safarar Ɗan-adam ta Amurka ta fitar, wanda ya zayyano ayyukan cigaba da ɗauka da amfani da ƙananan yara daga ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP a ƙasar Nijeriya.
A ranar 11 ga Oktoba ne aka wallafa rahoton, wanda ya ƙunshi ababen da ke faruwa daga ranar 1 ga Afrilun 2025 zuwa 31 ga Maris, 2026 kuma da ke wakiltar ƙoƙarin da Nijeriya take yi akan haramta ayyukan safarar ɗan-adam daga ma’aikatar Amurkan.
Ta sanya Nijeriya a jerin ƙasashe 14 da ke amfani da ko ɗaukar yara ƙanana aikin soja. Daga cikin ƙasashen akwai Rasha, Iran, Sudan ta Kudu da Somaliya da dai sauransu.
Rahoton ya kuma bayyana cewa ƙoƙarin Nijeriya wajen yaƙi da safarar, ya gaza cika sharuɗɗa da ƙa’idoji na tsawon shekaru 15 a jere. A cewar rahoton, gwamnatocin da aka sanya a jaddawalin na CSPA suna cikin halin yiwuwar a sanya musu takunkumin tallafin tsaro da lasisin siyan kayan aikin sojoji a shekara mai zuwa.
