
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wasu ‘yan bindiga sun halaka aƙalla mutane 20, ciki har da sojoji da ‘yan sanda bayan sun yi wa wata tawagar ƙananan ‘yan kasuwa da ke tafiya tare da rakiyar sojoji kwanton-ɓauna a Zamfara. Al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na ranar Asabar, a lokacin da ‘yan kasuwar suke kan hanyar tafiya daga yankin Gwashi zuwa kasuwar Nasarawa da ke Ƙaramar Hukumar Bukkuyum a cewar Reuters.
Wani ɗan yankin mai suna Musa Ɗanladi, wanda ya ce ya taimaka wajen ɗauko gawarwakin, ya shaida wa Reuters cewa, sojoji huɗu, ‘yan sanda uku da jami’in Sibil Difens suna daga cikin mamatan tare da wasu fararen hula guda 12.
Wata majiyar sojoji ta tabbatar da harin, inda ta ce mutane 19 sun jikkata. Saidai mahukuntan sojoji da ‘yan sanda ba su yi tsokaci ba a nan take game da labarin, kamar yadda Reuters ta ruwaito. Wannan al’amari ƙari ne akan adadin hare-hare da garkuwa da aka fuskanta a ‘yan watannin nan a jihar Zamfara, lamarin da ya ƙara jefa al’umma cikin fargaba game da amincin mazauna da matafiya a yankin.
A watan Satumba ne ‘yan bindiga suka sace wasu malamai shida akan hanyar Dakko-Damri da ke Ƙaramar Hukumar Bakura a jihar a lokacin da suke tafiya zuwa Talatan Mafara, kamar yadda Kakakin ‘yan sandan jihar, Yazid Abubakar ya shaida. Haka ma a Yuni, inda aka yi awon-gaba da ɗalibai guda bakwai a makarantar kwalejin tarayya (Federal Polytechnic) da ka Ƙaura Namoda, a gidajensu da ke unguwar Low-cost a garin Ƙaura Namoda.

