
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mai Shari’a Inyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya sanya ranar 20 ga watan Nuwamba, 2026 domin yin hukunci akan ƙorafin da ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar ya shigar, wanda ke neman a yi wa ƙararsa kwaskwarima akan Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC kan zargin shugaban Nijeriyar da amfani da takardar shaidar kammala hidimar ƙasa (NYSC) ta bogi.
Mai Shari’ar ya ayyana ranar ne bayan lauyan Atiku, Joseph Silas da lauyoyin ɓangaren waɗanda ake ƙara suka gabatar da ba’asinsu da tafka muhawara akan ƙarar.
Atiku da jam’iyyar ADC acikin ƙorafin nasu, sun roƙi kotun da ta soke cancantar Shugaba Tinubu da APC shiga zaɓen shugaban ƙasa na 2027, inda suka ƙalubalanci sahihancin takardar kammala NYSC da aka miƙa wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) a madadin shugaban.
Masu ƙarar, waɗanda suka shigar da ita akan Tinubu, APC da INEC, sun zargi jam’iyyar mai mulki da miƙa wa hukumar zaɓen takardar NYSC ta bogi, don haka suka nemi kotun da ta cire sunayen Tinubu da APC daga cikin jaddawalin ‘yan takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Saidai, ɓangaren masu kare ƙara sun shigar da ƙorafin ƙalubalantar matakin Atiku da ADC na neman izinin a yi wa ainihin ƙara tasu kwaskwarima, inda suka ce akwai rashin kiyaye wasu muhimman sharuɗɗa acikin wadda aka shigar da farko. Akan haka ne suka nemi kotun ta yi watsi da ita.
Bayan sauraron duka ɓangarorin, Mai Shari’a Ekwo ya ɗage zaman zuwa ranar 20 ga Nuwamba domin yanke hukunci a kai.
