
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ƙoƙarinta na ƙarfafa wa al’umma ta fuskar tattalin arziƙi, Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce ta amince da shirin siyan hannun jarin Rukunin Kamfanonin Ɗangote ga mazauna jihar su guda 36,176.
Shirin, a cewar Ma’aikatar Harkokin Jinƙai da Rage Raɗaɗi, an samar da shi ne da nufin bai wa mazauna ‘yan jihar damar shiga sahun masu hannun jari da kuma amfana da fannin kasuwancin ƙasar.
A ƙarƙashin wannan shiri, ana sa ran kowane mazauni ya samu jimillar hannun jari 20 a tsarin na Ɗangote Initial Public Officer (IPO), da haɗin-gwiwar ma’aikatun jinƙai da na kuɗin jihar, da kuma kamfanin zuba jari na Zamfara. Kwamishinan Harkokin Jinƙai, Salisu Musa Tsafe Kainuwa ne zai jagoranci aiwatar da shi.
Ma’aikatar ta ce, za a ɗauko waɗanda za su amfana da shirin ne daga faɗin ƙananan hukumomi 14 na jihar, inda za a bai kowace ƙaramar hukuma damar bayar da mutum 2,261, face Gusau, wadda aka ware wa mutum 4,522 a matsayinta na babban birni.
Ta bayyana cewa, wannan shiri zai haɗa da hatta masu nakasa domin tabbatar da damawa da kowane ɓangare na al’umma, tana mai cewa shirin ya samu amincewar Gwamna Dauda Lawal domin faɗaɗa damarmakin zuba jari da ƙarfafa wa ‘yancin cin gashin kai ta fuskar acikin al’umma.
