‘Yan Kamaru na jiran kwaskwarimar gwamnati bayan dawowar Shugaba Paul Biya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A kowane ƙarfe 5 na yammacin kowace rana Elvis Mbi na kunna rediyon gwamnatin ƙasa da tsammanin jin cewa Shugaba Paul Biya ka iya bayar da alamar amincewa sauya fasalin jagorancin siyasar Kamaru.

Paul Biya mai shekaru 93, ya dawo Kamaru ne a ranar 20 ga Agusta, bayan shafe kusan makonni 10 yana ƙasar waje. Tsawaita zamansa a can ya haifar da fara cece-kuce acikin al’umma akan halin lafiyarsa da inda yake, ciki har da wani iƙirari da ba a tabbatar ba na cewa ya rasu.

Har zuwa ranar 6 ga Oktoba, ba a samu sanarwar garambawul daga gwamnatin ƙasar ba bayan ‘yan ƙasar sun tsammaci haka. Haka kuma, an sake dawo da batun samar da mataimakin shugaban ƙasa a ƙarƙashin kundin tsarin mulkin ƙasar a Afrilu.

Mbi mai shekaru 39, ya shaida wa jaridar Al Jazeera cewa, “kowane ɗan Kamaru ya yi tsammanin bayan dawowarsa gida, zai canza gwamnati, amma babu wani abu har zuwa wannan lokacin.”

A ranar 31 ga Disambar 2025 ne Shugaba Biya ya yi wa ‘yan ƙasar alƙawarin kafa sabuwar gwamnati a ‘yan kwanaki masu zuwa. Bayan haka, sama da watanni tara ba a zartar da wannan alƙawari ba. Gurbin mataimakin shugaban ƙasa da ‘yan siyasa suka amince da rushewa a shekarar 1972 ya janyo hankalin jama’a musamman kan ganin buƙatar a dawo da shi acikin doka.

By Babaji

Leave a Reply