‘Yan bindiga sun kashe jami’in shige da fice a Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Rahotanni daga ƙaramar hukumar Dandi na nuna cewa safiyar yau Litinin waɗansu mahara da a ke sa ran lakurawa ne sun kai hari a wani shingen bincike na jami’an shige da fice da ke bakin garin Dole-Kaina a kan hanyar Kamba inda suka bindige jami’i ɗaya.

Wani jami’in shige da fice da bai so a bayyana sunan sa ba ya shaida wa wakilin mu da cewa ‘yan bindiga kan babura sun kai hari a shingen bincike kuma sun kashe ɗaya daga cikin jami’an da ke aiki wajen.
Ya ce bayan sun kashe shi sun gudu ba tare da ɓata lokaci ba a kan baburan su yayin da sauran jami’an da sauran ma’aikatan da ke aiki kan wannan hanyar suka gudu cikin jeji.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton dai babu wani bayani daga hukumar ko kuma hukumomin tsaro da ke da haƙƙin magana.

By ukarofi

Leave a Reply