Hukumar ƙwallon ƙafar Portugal ta dakatar da Ronaldo na wata guda kan barin tawagar ‘yan wasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar kula da Harkokin Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasar Portugal (FPF) ta dakatar da Kyaftin ɗin tawagar ‘yan wasanta kuma zakaran ɗan ƙwallon ƙafar duniya, Cristiano Ronaldo na tsawon kwana 30 da cin sa tarar Yuro 255 bayan ya fice ɗaga tawagar a lokacin da take karɓar horo a Birnin Copenhagen na ƙasar Denmark ba tare da izini ba sakamakon wata rashin jituwa da koci Jorge Jesus.

Al’amarin ya faru ne a ranar 30 ga Satumba a lokacin da ɗan wasan mai shekaru 41 ya bar tawagar gabanin wasan ƙasarsa da Denmark. Wannan mataki ya faru ne yayin da aka samu ƙamarin fargaba kan rawar da yake takawa a tawagar da kuma yadda ake gudanar da wata yarjejeniya da ya ce ya cimma da koci Jesus kan shigarsa wasannin Portugal.

Barin Ronaldo cikin ‘yan wasan ya janyo FPF ta ɗauki matakin ladabtarwa akansa inda da fari ta masa dakatarwar kare ƙamarin rikicinsa da kociyan yayin da ta fara bincike a kai. Kwamitin ladabtarwar hukumar daga bisani ya yanke hukuncin horar da shi, kamar yadda rahotanni suka bayyana a ranar Litinin.

Rikici tsakanin mutanen biyu ya soma ne a lokacin da Portugal take buga wasannin ƙasa-da-ƙasa, inda aka bar Ronaldo a benci a wasan ƙasar da Norway duk da cewa ya fito ya yi atisaye na tsawon lokaci. Portugal ta yi nasara a wasan na ranar 27 ga Satumba da ci 2 da 1 amma Ronaldo bai buga ba. Wannan al’amari ya fusata ɗan wasan musamman ganin yadda hakan ya saɓa wa yarjejeniyarsa da kociyan tawagar.

Fargabar ta ƙaru ne gabanin wasan Portugal na gaba a lokacin da Jesus ya yi wa manema labarai bayani kan al’amarin, inda Ronaldo ya yi iƙirarin cewa jawabin nasa ya saɓa wa ainihin abin da suka tattauna a ɓoye. Bayan binciken da kwamitin FPF ya gudanar, an dakatar da kyaftin ɗin na tsawon wata guda da kuma tilasta masa biyan tarar €255, kamar yadda rahotanni suka bayyana a ranar 19 ga Oktoba.

By Babaji

Leave a Reply