Daga AISHA ASAS
Annabin rahma (S.A.W) ya yi bayanin cewa ana neman mace saboda abubuwa da huɗu, ciki har da dukiyarta, kyawunta da addininta, sannan ya koyar da a fifita mai addini.
Domin mace ta gari ce za ta iya zama tushen kwanciyar hankali a gida, ta taimaka wajen gina iyali, kuma sama da komai, ta kasance uwa ga ‘ya’yan da za a haifa.
A yau darasinmu na iyali zai karkata ne kan maza, tun daga samarin da ba su yi aure ba zuwa magidanta da ke shirin ƙarin aure. Domin kuwa, akwai wani kuskure da maza da dama ke yi tun kafin su kafa gida, kuskuren da daga baya zai iya zama abin da za su dinga fama da shi a cikin gidajensu da tarbiyyar ‘ya’yansu.
Da yawa daga cikin maza abin da suka fi kallo a matar da za su aura ba shi ne abin da zai fi tasiri a zaman aurensu ba. Duk da cewa malamai a kullum suna faɗakarwa da irin matan da ya kamata a aura, wasu kan fi karkata ga kyau, matsayi ko dukiya, su manta da halayen da za su zauna da su tsawon rayuwa. Rashin kula da wannan darasi ba zai cutar da kai kaɗai ba, zai iya shafar ‘ya’yanka, matar da ka aura, har ma da al’ummar da waɗannan ‘ya’yan za su tasiri a gaba.
To, ta yaya matar da za ka aura za ta iya cutar da kai, ‘ya’yanka da ita kanta?
Mace ta gari ce ta san muhimmancin sauke haƙƙoƙin mijinta da ke kanta. Ita ce za ta iya mayar da gidanka muhalli na kwanciyar hankali, wurin da za ka samu natsuwa bayan ka fuskanci gajiyar rayuwa da neman abin da za a ci.
Ita ce za ta rufa asirinka, domin ba wadda ta san ka kamar ita. Za ta san gazawarka, amma ba ta mai da su abin da za ta watsa wa mutane a matsayin labari ba. Za ta yi haƙuri da kai a lokacin da abubuwa ba su tafi yadda ake so ba. Da waɗannan misalai kawai, mutum zai iya fahimtar yadda zaɓin mace yake da muhimmanci ga rayuwar namiji.
Sai mu dawo ga ‘ya’yanka.
Ba kowanne yaro ne yake samun irin tarbiyyar da ake fata ba. Akwai yaran da yanayin gidan da suka taso a cikinsa ke taka muhimmiyar rawa wajen yadda za su fahimci rayuwa da mu’amala da mutane. Kuma idan ka bi tushen tarbiyyar yaro, za ka ga cewa uwa tana da babban matsayi a cikinsa.
Na san akwai waɗanda ake jarrabawa ta ɓangaren ‘ya’ya, ta hanyar samun yara masu wahalar tarbiyya ko halaye da ba su yi daidai da abin da iyaye suke fata ba. Wannan ma jarabawa ce da Allah ke yi wa bayinsa. Amma akwai kuma yaran da matsalar tarbiyyarsu ta samo asali ne daga rashin ingantacciyar tarbiyya tun daga gida.
Uwa ta gari ce za ta fara koyar da ‘ya’yanta da halayyarta kafin ma ta fara koyar da su da baki. Irin zaman da take yi da mijinta, irin yadda take mu’amala da mutane, yadda take magana, yadda take fushi da yadda take warware matsaloli, duk suna zama darasi a gaban ‘ya’yanta.
Har wa yau, uwa ta gari ce za ta damu da sallolin ‘ya’yanta, karatunsu, abokantakarsu da kuma yadda suke mu’amala da mutane. Ba wai za ta jira sai yaron ya girma sannan ta fara tunanin gyaransa ba. Tarbiyya tana farawa tun lokacin da yaro bai ma san abin da ake kira tarbiyya ba.
Ya kai maigida, ka sani cewa duk irin ƙoƙarin da za ka yi wajen gina ‘ya’yanka kan turba madaidaiciya, ba zai zama cikakke ba idan mutumin da yake tare da su mafi yawan lokuta bai fahimci nauyin da ke kansa ba. Idan ka gina, ita tana rushewa; idan ka koyar, ita tana warware abin da ka koyar, aikin tarbiyyar zai zama kamar mutum yana ɗinka riga ne ana yage masa daga gefe.
A taƙaice dai, uwa ita ce makarantar farko ga ‘ya’yanta. Idan kuwa ba ka nemo musu wadda za ta iya koya musu kyakkyawa, ta hana su mummuna, ta nuna musu darajar addini da mutunci ba, to ka sani cewa ba su kaɗai za su fuskanci sakamakon hakan ba. Kai ma za ka fuskanta, domin waɗannan yaran su ne mutanen da za su girma su zama wani ɓangare na al’umma.
Sai kuma matar da kanta.
Na san za ka ce, idan mutum ya auri macen da ba ta da kyawawan halaye, ai ita ma za ta shiga cikin matsalar. Haka ne. Amma abin da ya kamata namiji ya fahimta shi ne, aurensa da mace ba kawai neman wadda zai zauna da ita ba ne; wani nauyi ne da zai iya taimaka mata ta ƙara gyaruwa ko kuma ya sa ta ci gaba da zama a kan abin da bai dace ba.
Idan har maza za su guji auren macen da ba ta da kyawawan halaye, wataƙila hakan zai sa wasu daga cikin matan su tsaya su tambayi kansu: me ya sa ake guje masu? Me ya kamata in gyara a halayyata? Amma idan ana ci gaba da aurensu ba tare da an damu da waɗannan abubuwan ba, za su iya rayuwa cikin tunanin cewa babu wata matsala a tare da su, har su rasa damar gane aibin da ke buƙatar gyara.
A nan ne namiji yake da wani nauyi mai girma: kada ya bari sha’awar aure ta rufe masa ido daga abubuwan da za su iya shafar rayuwarsa da rayuwar ‘ya’yansa.
Annabin rahma (S.A.W) ya kuma koyar da muhimmancin zaɓen ma’aurata masu kyakkyawar dabi’a da addini. Don haka, idan za ku yi aure, kada ku bari kyau, matsayi ko dukiya su zama dalilai mafi rinjaye a zaɓinku. Waɗannan abubuwa suna da nasu matsayi, amma idan aka ɗora su a gaban addini da halayya, nadama na iya biyo baya.
Ku yi wa ‘ya’yanku adalci tun kafin ku haife su.
Domin zaɓin matar da za ta haife su, ta raina su, ta koyar da su, ta zauna tare da su a mafi yawan lokutan rayuwarsu, wani ɓangare ne na zaɓar irin yanayin da za su girma a cikinsa.
Ƙarancin uwaye masu tarbiyya da ilimin addini na daga cikin abubuwan da ke iya raunana tarbiyyar yara da kuma barin gibi da wasu abubuwa marasa kyau za su iya cikewa. Uwa tana da babban kaso a rayuwar ɗanta, don haka iliminta da halayyarta ba abin da ya tsaya a cikin gida kaɗai ba ne; haske ne ko duhu zai iya wucewa daga gida zuwa al’umma, saboda ita ce makaranta ta farko ga ɗanta.
Kuma kamar yadda ake cewa, karatun ƙaramin yaro tamkar rubutu ne a dutse. Abin da aka fara zana masa tun yana ƙarami kan yi wuya a goge shi. Ana iya ƙara wani abu a kansa, ana iya gyara shi, amma abin da aka fara gina shi a kai zai ci gaba da kasancewa wani ɓangare na rayuwarsa.
Shi ya sa, namiji kafin ya zaɓi matar da zai aura, ya kamata ya tuna cewa ba kansa kaɗai yake zaɓa wa abokiyar rayuwa ba. Yana kuma zaɓa wa wasu ‘ya’yansa da ba su zo duniya ba ne, waɗanda za su girbe abinda zaɓin nasa ya shuka har tsawon rayuwarsu.
Uwa ita ce makarantar farko ga ‘ya’yanta. Don haka, zaɓin uwa shi ma zaɓin irin makarantar da za a fara gina rayuwar ‘ya’yanka a cikinta ne.
