
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kwamitin yaƙi da yaɗuwar cutar Ebola da wasu barazanar lafiya na Shugaban ƙasa, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa yana da ƙarfin daƙile annobar Ebola a ƙasar, yana mai cewa ana ɗaukar dukkan matakan da suka dace don daƙile yaɗuwarta acikin al’umma. Shugaban kwamitin kuma Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila ne ya bayar da wannan tabbaci yayin ganawa da manema labarai bayan zaman gaggawa da kwamitin ya gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Laraba.
Gbajabiamila ya ce, kwamitin ya kasance yana aiki a bayan fage tun sadda aka ƙaddamar da shi a Yunin wannan shekarar, yana mai ƙarawa da cewa yunƙurin nasu ya taimaka wajen gano ɓullar cutar a ranar Talata. “Yana da muhimmanci al’umma ta sani cewa tun lokacin da batun Ebola ya taso a Yuni, an sanya ido kan kusan jiragen sama 44,000 a ciki da wajen Nijeriya. Don haka, saboda abin da Ma’aikatar Lafiya, kwamitin yaƙin da dukkan hukumomi suke yi ne. Kowane ɓangare na taka muhimmiyar rawa a kai,” inji shi.
Ya bayyana cewa, saboda ƙoƙarin ɓangarorin ne ya sa aka gano cewa matar da ta je Abuja tana ɗauke da cutar cikin ƙanƙanin lokaci duk da cewa a lokacin da ta shigo Nijeriya babu wata alama da aka gani na cutar a tare da ita. A cewarsa, wannan ya nuna yadda ƙasar ta kimtsa wa tunkarar cutar, kamar yadda ya bayyana a wata sanarwa da Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya fitar a ranar Laraba.
Gbajabiamila ya kuma tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa kwamitin zai ƙarfafa dukkan matakan da ake buƙata don ganin an daƙile yaɗuwar cutar acikin al’ummar ƙasa, yana mai kira a gare su da su bayar dukkan goyon baya da haɗin kai ga hukumomin lafiya, musamman kan kiyaye sharuɗɗan samun kariya daga kamuwa da cutar. A ranar Talata Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da ɓullar cutar a karon farko a Abuja bayan an gano cewa wata mata da ta zo Nijeriya daga Uganda tana ɗauke da ita.
Ministan Lafiya da Walwalar Al’umma, Farfesa Ali Pate, wanda ya sanar da labarin, ya ce an gano wasu mutane 44 da ke ɗauke da alamun cutar, waɗanda aka ware su kuma ake kula da su, ciki har da ma’aikatan lafiya, marasa lafiya, masu aikin raino da wasu mutanen da ake zargin sun shigo Nijeriya tare da matar.
