Tsaro: Gwamna Sule ya yaba wa DSS kan kame masu safarar makamai a Nasarawa

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafia

Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi A. Sule ya yaba wa hukumar tsaro ta farin kaya DSS kan cigaba da farmakin da take yi kan ‘yan fasa-ƙwauri da masu safarar makamai a jihar.

Yabon ya biyo bayan kame wata matashiya ‘yar shekara 23 da ake zargi da safarar makamai wato Aisha Mohammed mazauniyar Bwari a babban birnin tarayya Abuja wadda aka kama a Keffi.

Wanda ake zargin wadda ke tsare a halin yanzu an kama ta ne ɗauke da harsasai 202 kirar 7.62mm da mujallu uku marasa komai a ciki.

A cewar wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labarai na Gwamnan Ibrahim Addra ya fitar a yau Alhamis, sauran waɗanda ake zargi da safarar makaman da aka kama tsakanin watan Agusta da Satumba na 2026 sun haɗa da Hassan Sani mai shekara 40 da Abdulkadir Idrissa mai shekara 41 da Salihu Garba mai shekara 70 wanda aka fi sani da Nabayi.

Yace an ƙwato harsasai 678 kirar 7.62mm da 99 kirar 7.5mm tare da wasu kayayyaki daga hannun waɗanda ake zargin.

A wani samame kuma a watan Agusta na 2026 an kama wani mai safarar makamai mai suna Ismail Lawalli ɗan asalin Jihar Zamfara a kan babbar hanyar Keffi zuwa Abuja ɗauke da harsasai 1,262 kala-kala.

Gwamna Sule ya yaba da jajircewar jami’an DSS da sauran hukumomin tsaro na jihar wajen sauke nauyin da ke kansu.

Ya kuma yaba da hadin kai da jajircewar hukumomin tsaro da gwamnatinsa, inda ya yi alƙawarin cigaba da ba su dukkan goyon bayan da ake buƙata domin gudanar da aikinsu.

Gwamnan daganan sai ya tabbatar wa al’ummar jihar baki ɗaya aniyarsa ta magance masu aikata laifuka da miyagun ayyuka tare da neman goyon bayan kowa da kowa.

By ukarofi

Leave a Reply