EU ta bai wa Nijeriya yuro miliyan 20 tallafin tsaro

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta amince da bai wa Nijeriya tallafin tsaro na yuro miliyan 20 — kwatankwacin fiye da naira biliyan 29 — domin ƙarfafa ayyukan rundunar sojojin ƙasar da kuma inganta haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu.

Jakadan  Tarayyar Turai a Nijeriya, Gautier Mignot, ya ce tallafin zai kasance ƙarƙashin shirin samar da zaman lafiya na ƙungiyar, wanda aka tsara domin tallafa wa ƙoƙarin Nijeriya na shawo kan matsalolin tsaro.

Tallafin na cikin shirye-shiryen haɗin gwiwa tsakanin EU da Nijeriya na bunƙasa zaman lafiya da tsaro, musamman a yankunan da ke fama da tashe-tashen hankula.

Sai dai ba za a miƙa kuɗin ga gwamnatin Nijeriya kai tsaye ba, inda ake sa ran za a yi amfani da su wajen samar da kayan aikin soji na zamani, ciki har da jiragen yaƙi masu saukar ungulu da jiragen sama marasa matuƙa.

Shugaban cibiyar nazarin tsaro da bayanan sirri ta Beacon Consulting, Dakta Kabiru Adamu, ya bayyana cewa irin wannan tallafi na iya taimaka wa wajen inganta ayyukan soji, matuƙar an yi amfani da shi yadda ya kamata.

Tallafin ya zo ne a daidai lokacin da Nijeriya ke ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsaro a sassa daban-daban na ƙasar, lamarin da ke ƙara buƙatar ingantattun kayan aiki da dabarun yaƙi domin tunkarar matsalolin.

By ukarofi

Leave a Reply