Amurka ta jinjina wa Nijeriya kan yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kasar Amurka ta yaba wa Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) bisa nasarar da ta samu wajen gano cibiyoyin sarrafa miyagun ƙwayoyi da ’yan ƙasar Meɗico ke gudanarwa a Nijeriya, tare da hukunta waɗanda aka samu da laifi.

Muƙaddashin Sakataren Amurka mai kula da yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Afirka da Gabas ta Tsakiya, Michael Gonzales, ne ya bayyana hakan yayin ziyarar da ya kai wa shugaban NDLEA, Janar Muhammadu Buba Marwa mai ritaya, a ofishinsa.

Gonzales, wanda ya fara aiki makonni huɗu da suka gabata, ya ce ya zaɓi Nijeriya a matsayin ƙasa ta farko da zai ziyarta saboda rawar da NDLEA ke takawa wajen yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi da sarrafa su ba bisa ƙa’ida ba.

Ya bayyana cewa ya kai ziyarar ne domin sanin dabarun da hukumar ke amfani da su wajen ganowa da dakile ayyukan masu safarar miyagun ƙwayoyi, yana mai cewa nasarorin da take samu abin a yaba ne.

Jami’in ya kuma jinjina wa Buba Marwa bisa jagorancinsa, wanda ya ce ya taimaka wajen samun nasarorin da suka zama abin koyi ga sauran ƙasashe.

Gonzales ya bayyana gano cibiyoyi huɗu da ake sarrafa sinadarin methamphetamine a Nijeriya a matsayin babbar nasara da ke nuna ƙwarewa da jajircewar jami’an NDLEA.

Ya ce sinadarin methamphetamine na daga cikin miyagun ƙwayoyin da ke haifar da babbar illa a Amurka, saboda haka ƙasar ke ƙara ƙaimi wajen yaƙi da safararsa a faɗin duniya.

A nasa jawabin, Marwa ya yaba wa gwamnatin Amurka bisa haɗin gwiwar da take bai wa Nijeriya wajen yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi, wanda ya bayyana cewa yana da mummunar illa ga al’umma, musamman matasa.

Ya ce masu aikata laifuffuka ba sa la’akari da iyakokin ƙasashe, don haka yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi na buƙatar haɗin gwiwar ƙasashen duniya, kamar yadda ake yi wajen yaƙi da makamai da ta’addanci.

Marwa ya bayyana ayyukan ’yan ƙasar Meɗico da ake zargi da sarrafa miyagun ƙwayoyi a Nijeriya a matsayin babbar barazana ga tsaron ƙasa.

Ya ce hukumar ta gano wata cibiyar sarrafa miyagun ƙwayoyi a dajin Ijebu da ke Jihar Ogun, inda ta kama ’yan Meɗico uku tare da sinadarin da darajarsa ta kai dala miliyan 360.

Ya ƙara da cewa bayan makonni huɗu, jami’an hukumar sun sake kai samame wata cibiyar sarrafa miyagun ƙwayoyi a ƙauyen Tapa da ke Jihar Ogun, inda suka kama wani ɗan ƙasar Meɗico.

Haka kuma, hukumar ta lalata wasu cibiyoyi biyu a jihohin Enugu da Ebonyi.

A cewar Marwa, ana zargin masu gudanar da cibiyoyin ba sa sarrafa miyagun ƙwayoyin domin kasuwar cikin gida ta Nijeriya kawai, sai dai suna sarrafa su ne domin safarar su zuwa wasu ƙasashe na duniya.

By ukarofi

Leave a Reply