
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Iyalan marigayin jagoran Afenifere, Pa Reuben Famuyide Fasoranti, sun ayyana ranakun 17 da 18 ga watan Disambar 2026 a matsayin lokacin jana’izarsa yayin da aka fara shirye-shiryen karrama babban ɗan ƙasar bisa gudummawarsa ga al’umma.
‘Yarsa, Olufubmilayo Fasoranti ce ta sanar da ranakun jana’izar a lokacin da ta karɓi baƙuncin ‘yan tawagar ɗaliban farko na makarantar Anglican Grammar School da ke yankin Iju-Itaogbolu na Jihar Ondo, waɗanda suka ziyarci iyalan domin jajenta musu kan rashin tsohon shugaban makarantar tasu.
Wannan ziyara ta bayar da dama ga tsofaffin ɗaliban domin su isar da girmamawarsu ga iyalan bisa karamcin marigayin da ya kasance shugaban makarantar a lokacin da suke ɗalibanta.
Olufunmilayo ta bayyana cewa iyalan suna ƙoƙarin ganin an yi jana’izar ne kafin ƙarshen 2026, bisa la’akari da zaɓukan 2027 da ke tafe da kuma bukukuwan ƙarshen shekera. Ta kuma ce za a yi taron janazar ne a Cocin St. David’s Anglican Cathedral da ke birnin Akure a Jihar Ondo, inda marigayin ya kasance yana zuwa gudanar da harkokin addini.
