2027: Jaddawalin rajistar masu zaɓe a jihohi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Yayin da zaɓukan shekarar 2027 ke cigaba da ƙaratowa, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanar da fitar da jaddawalin rajistar masu zaɓe a faɗin Nijeriya, waɗanda adadinsu ya kai guda 103,428,715 inda arewa ta samu sama da kaso 54 na jimillarsu.

Yadda bayanin adadin yake a sassan shiyyoyi shida na Nijeriya ya nuna cewa, Arewa tana da rajistar masu zaɓe 56,014,673, wanda ke wakiltar jimillar kaso 54.16 a matakin ƙasa, yayin da kudu take da masu rajista 47,414,042 ko kaso 45.84. Bambancin shi ne masu zaɓe 8,600,631, wanda ke nuna cewa arewa ce ke da kaso mafi girma na masu zaɓe yayin da jam’iyyu da ‘yan siyasa suke shirin tunkarar babban zaɓen 2027.

Adadin da INEC ta fitar ya bayar da muhimmin yanayin masu zaɓe gabanin zaɓukan na 2027, saidai hakan ba shi ke nuna yawan adadin da wata jam’iyya ko wani ɗan takara zai samu ba duk yawan adadin masu rajistar.

Shiyyar Arewa maso Yamma ita ce kan gaba da rajistar masu zaɓe guda 25,083,411, wanda ke wakiltar kashi 24.25 daga baki ɗaya adadin a matakin ƙasa. Sai Kudu maso Yamma mai masu rajista 19,614,274 ko kaso 18.96, yayin da Arewa ta Tsakiya take da 16,965,787 da ke wakiltar kaso 16.40. Ita kuwa Kudu maso Kudu da ta zo ta huɗu, tana da rajistar mutum 15,823,550 ko kaso 15.30, yayin da Arewa maso Gabas ke da 13,965,475, mai wakiltar kaso 13.50. Sai Kudu maso Gabas mai rajista 11,976,218 ko kaso 11.58 na baki ɗaya adadin.

Legas, Kano da Kaduna ne suka fi yawan rajista a matakin jihohi, inda Legas take da 7,488,633, sai Kano mai 6,570,276 da Kaduna mai rajistar 4,662,640. Hakan na nufin suna wakiltar kaso 18.1 daga baki ɗaya rajistar. Sannan Jihar Katsina ce ke biye da su da rajistar 3,876,051, yayin da Ribas take da 3,736,434. Oyo tana da 3,588,111, Delta mai 3,525,988, Benue tana da 3,057,225, Ogun 3,037,981 da kuma Bauchi mai guda 3,012,547.

A baya-bayan dai an riƙa samun raguwar adadin masu zuwa kaɗa ƙuri’a a zaɓukan shugaban ƙasa daga kaso 53.68 a 2011 zuwa kaso 43.65 a 2015, zuwa kashi 34.75 a 2019 da kuma kaso 26.71 a 2023, kamar yadda tarihin adadin masu zaɓe ya nuna daga kafafen yaɗa labarai.

By Babaji

Leave a Reply