Daga AISHA ASAS
Akwai kalaman da iyaye kan furta da kyakkyawar niyya, suna ganin cewa suna ƙarfafa ’ya’yansu ne su zama mutanen kirki, amma ba su san cewa kalaman na iya zama sanadin raunin zuciyar yaran da suke ƙoƙarin gyarawa ba. Wani lokaci, yaro zai yi ƙoƙari iya ƙarfinsa, ya yi abin da yake ganin zai faranta wa iyayensa rai, amma maimakon a yaba masa ko a nuna masa inda ya kamata ya ƙara ƙoƙari, sai ya ji an kawo wani yaro an ɗora shi a kansa, kamar dai ƙoƙarinsa bai da wani amfani.
“Dubi ɗan wane, ka ga yadda yake karatu. Kai kuwa kullum sai an gaya maka abu ɗaya sau goma” “Dubi ’yar wance, ta iya girki, ta iya gyaran gida, ke kuwa ba kya iya komai”
Waɗannan kalamai na iya zama kamar ƙananan maganganu ne a kunnen wanda ya furta su, amma ga yaron da ake gaya wa, suna iya zama saƙon cewa shi bai kai matsayin da iyayensa suke so ba, kuma komai ƙoƙarinsa, akwai wanda zai fi shi a idon waɗanda ya fi son su yaba masa.
Abin takaici, wasu iyaye ba sa lura da cewa idan suka ci gaba da amfani da kwatantawa a matsayin hanyar tarbiyya, za su iya jefa ’ya’yansu cikin gasa marar amfani, hassada, rashin yarda da kai da kuma tunanin cewa ƙaunar iyaye tana dogara ne da abin da mutum ya iya yi.
Kowanne yaro yana da irin tasa baiwar:
Ya kamata iyaye su fahimci cewa yaran da suka haifa, ko da kuwa suna da uwa da uba ɗaya, ba lallai ne su kasance da hali iri guda ba, saurin fahimta iri ɗaya ko baiwa iri ɗaya ba. Wani yaro zai iya zama mai saurin fahimtar darasi a makaranta, wani kuma ya fi ƙwarewa wajen warware matsaloli ko gudanar da ayyukan hannu. Wani yana iya zama mai yawan magana da bayyana ra’ayinsa, yayin da wani yake buƙatar lokaci kafin ya samu ƙarfin gwiwar faɗin abin da yake tunani.
Haka kuma, akwai yaron da yake iya yin abubuwa cikin sauri, akwai kuma wanda yake buƙatar a yi masa bayani sau da dama kafin ya fahimta. Wannan ba yana nufin cewa na biyun ba shi da hankali ko ba zai iya samun nasara ba. Abin da yake nufi shi ne cewa akwai bambancin da ya kamata iyaye su fahimta, su kuma taimaka wa kowane yaro ya bunƙasa bisa irin baiwar da yake da ita.
Idan yaro yana fama da wani fanni, aikin iyaye shi ne su gano abin da yake hana shi samun ci gaba, su taimaka masa ya shawo kan matsalar, maimakon su riƙa nuna masa wani yaro a matsayin ma’aunin abin da ya kamata ya zama. Wataƙila yaron yana buƙatar ƙarin kulawa, wataƙila yana fama da matsalar fahimtar wani darasi, ko kuma akwai wata damuwa da yake ɗauke da ita wadda iyayensa ba su sani ba.
Saboda haka, kafin iyaye su yanke hukuncin cewa ɗansu ya gaza, ya kamata su fara tambayar kansu ko sun fahimci yanayin da yake ciki, da kuma irin taimakon da yake buƙata domin ya inganta.
Kwatantawa na iya haifar da abin da iyaye ba su yi tsammani ba:
Wani abin da ya kamata iyaye su lura da shi shi ne cewa ba duk yaron da ya yi shiru bayan an kwatanta shi da wani ne ya amince da abin da aka gaya masa ba. Wasu yara suna jin zafi ne a zuciyarsu, amma ba su da ƙarfin bayyana shi. Wasu kuma sukan fara ganin kansu a matsayin marasa amfani, musamman idan kwatantawar ta zama ruwan dare a gidansu.
Idan aka saba gaya wa yaro cewa wani ya fi shi, zai iya fara yarda da wannan tunanin, har ya daina ƙoƙarin inganta kansa. A maimakon ya ga kuskure a matsayin damar koyo, sai ya riƙa ganin sa a matsayin wata shaida cewa ba shi da ƙwarewa. Wannan na iya rage masa ƙarfin gwiwar gwada sababbin abubuwa, ko kuma ya sa ya daina bayyana abin da yake so saboda tsoron kada a sake kunyata shi.
Akwai kuma yaran da kwatantawar ke sa su fara ƙin ’yan uwansu ko yaran da ake amfani da su wajen auna ƙimar su. Yaron da a kullum ake gaya masa cewa ɗan uwansa ya fi shi, zai iya fara kallon ɗan uwan a matsayin kishiya, maimakon ya gan shi a matsayin wanda za su iya taimaka wa juna su ci gaba.
A irin wannan yanayi, abin da ya kamata ya zama ƙauna da haɗin kai a tsakanin yara zai iya rikiɗewa zuwa gasa, fushi da ɓacin rai. Kuma idan iyaye ba su lura da abin da ke faruwa ba, za su iya ɗauka cewa yaran suna saɓani ne kawai, alhali salon tarbiyyar da ake amfani da shi a gidan na iya zama ɗaya daga cikin abubuwan da ke ƙara rura wutar rashin jituwa.
Shin yabon yaron da ya yi bajinta laifi ne?
Za mu ci gaba a mako mai zuwa.
