Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina ya buƙaci al’ummar Shiyyar Funtua da jihar Katsina baki ɗaya su sabunta wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC wa’adin mulki a zaɓen 2027, domin ci gaba da samun ci gaba da wadata.
Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya bayyana haka ne lokacin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen Tinubu/Dikko na 2027 a Funtua, inda ya ce taron ya kuma kasance wata dama ta gabatar da nasarorin gwamnatinsa ƙarƙashin shirin Building Your Future Agenda.
Gwamna Raɗɗa ya ce tsaro na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta mayar da hankali a kai, tare da jaddada cewa zaman lafiya shi ne ginshiƙin noma, ilimi da harkokin kasuwanci.
Ya kuma bayyana ayyukan raya hanyoyi, garuruwa da samar da makamashi, musamman a Funtua inda ya ce gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa manoma, masu matsakaita da kananan sana’o’i, mata da matasa, tare da inganta ilimi, kiwon lafiya da inshorar lafiya ga masu rauni.
Gwamnan ya yaba wa Shugaban Kasa Tinubu kan sauye-sauyen Renewed Hope Agenda, tare da tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar Katsina za ta ci gaba da haɗa kai da Gwamnatin Tarayya domin ƙara tasirin shirye-shiryen gwamnatin tarayya a Katsina.
Ya kuma buƙaci ‘yan takarar APC da masu ruwa da tsaki su gudanar da kamfe cikin lumana, ladabi da haɗin kai, tare da ƙarfafa hulɗa da al’umma a ƙananan hukumomi 34 da mazaɓu 361.
A nasa jawabin, darakta-janar na kwamitin yaƙin neman zabe na Tinubu/Dikko 2027, Arc. Ahmed Musa Dangiwa, ya yaba wa al’ummar Shiyyar Funtua akan yadda suka fito dafifi, yana mai cewa Tinubu na farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa, yayin da Raɗɗa ke kawo ci gaba a matakin ƙasa.
Tun farko a jawabinshi, Shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina, Dr. Bishir Gambo Slaulawa, ya bayyana taron a matsayin nuna ƙarfin jam’iyyar, inda ya miƙa tutoci ga ‘yan takarar kujerun sanatoci uku, ‘yan majalisar wakilai 15 da ‘yan majalisar dokokin jiha 34, tare da umartar su da su fifita muradun jama’a.
