Abin da ya sa farashin CNG ba zai tashi ba – Gwamnatin Tarayya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shirin Shugaban ƙasa na Bunƙasa Amfani da Iskar Gas ɗin CNG da Motocin Lantarki (PI-CNG&Eɓ) ya tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa babu dalilin fargabar tashin farashin gas ɗin CNG a faɗin ƙasar.

Babban Jami’in Gudanarwa na shirin, Tosin Coker, ne ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da manema labarai da aka gudanar a Kano ranar Alhamis. Coker ya ce, Nijeriya na da isasshen iskar gas, kuma ana ƙayyade farashin CNG a cikin gida, saɓanin man fetur wanda farashinsa ke sauyawa bisa yanayin kasuwar duniya da kuma tasirin rikice-rikicen siyasa da na ƙasashen duniya.

Ya bayyana cewa bai kamata ’yan Nijeriya su yi tsammanin farashin CNG zai riƙa tashi daidai da yadda farashin man fetur ke tashi ba, domin akwai bambanci tsakanin yadda ake samar da iskar gas da yadda ake sayar da man fetur a kasuwannin duniya. A cewarsa, Nijeriya na da wadataccen iskar gas, kuma ƙasar na da ikon sarrafa farashinta, yayin da farashin man fetur ke dogara da abubuwan da ke faruwa a duniya. Coker ya ce, “Kada mutane su ji tsoron cewa farashin CNG zai tashi yana bin sawun farashin man fetur. Dalili kuwa shi ne, CNG iskar gas ce ta halitta, kuma muna da ita a yalwace.

A matsayinta na ƙasa, muna da ikon sarrafa farashinta. Amma farashin man fetur ana ƙayyade shi ne a kasuwannin duniya, don haka rikice-rikicen siyasa da sauran abubuwan da ke faruwa tsakanin ƙasashe na iya shafar farashinsa.”

Ya ƙara da cewa, rikicin da ya ɓarke a Iran ya taimaka wajen haddasa tashin farashin man fetur, haka kuma farashin iskar gas ɗin girki mai ruwa (LPG) ya ƙaru. A cewarsa, farashin LPG na bin sauye-sauyen farashin man fetur ne saboda yadda ake samar da shi, saɓanin iskar gas mai ruwa ta musamman (LNG) da kuma iskar gas ɗin CNG.

Coker ya kuma bayyana cewa yayin da amfani da CNG ke ƙaruwa a Nijeriya, babu wani dalili na zahiri da zai sa farashinsa ya tashi a nan gaba. Maimakon haka, ya ce akwai yiwuwar farashin ya ragu sakamakon ƙaruwa da gasar kasuwanci tsakanin masu samar da shi. Ya ce, a nan gaba, ’yan Nijeriya da dama za su rungumi amfani da CNG, lamarin da zai ƙara yawan masu samar da shi da kuma ƙarfafa gasa a kasuwa, wanda zai taimaka wajen rage farashin.

By ukarofi

Leave a Reply