
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Northern Youth Frontiers (NYF), wadda haɗakar ƙungiyoyin matasan arewacin Nijeriya ce, ta yi kira da a gaggauta ɗaukar mataki akan kisan Sheikh Yahaya Masussuka da aka aiwatar a Ƙaramar Hukumar Dutsin-Ma da ke Jihar Katsina makon da ya gabata.
Ta kuma yi tsokaci kan zuwa Umara da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi a kwanan nan, inda ta yaba masa bisa zuwa ƙasa mai tsarki domin neman taimakon Allah (SWT) wajen gudanar da harkokin ƙasa.
NYF ta bayyana kisan malamin a matsayin barazana ga haɗin kan ƙasa da zaman lafiyarta, inda ta buƙaci hukumomin tsaro da su tabbatar da kamawa da gurfanar da dukkan masu hannu aciki domin su fuskanci hukuncin da dokar ƙasa ta tanada.
Shugaban ƙungiyar, Sama Musa ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar, inda ya jaddada muhimmancin girmama addinan juna a zamantakewa, addu’o’i da ƙoƙarin gudanar da muhimman ayyuka tare don ci-gaban ƙasa. Ya ce, bambance-bambancen yare, al’ada da addini na buƙatar fahimtar juna da zaman lafiya acikin ‘yan ƙasa.
Ƙungiyar ta yi kira ga Shugaba Tinubu, Sufeto-Janar na ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su ƙaddamar da aikin bincike mai zurfi kan kisan tare da tabbatar da gurfanar da dukkan masu aciki a gaban doka. A cewarta, kisan malaman addini da wasu ‘yan ƙasa marasa laifi da ake yi ka iya zurfafa ƙiyayya da rashin tsaro muddin ba a hukunta masu hanu a laifin ba.
A ƙarshe, ta jaddada ƙoƙarinta na cigaba da tallafa wa shirye-shiryen samar da haɗin kai, tsaro, girmama addini da zaman lafiya a sassan Nijeriya a matsayin ababen da suka dace a fifita domin ɗorewar al’amura da ci-gaban ƙasa.
