
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC, ta cire sunan ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo daga cikin jaddawalin sunayen ‘yan takarar da ta sabunta domin zaɓukan 2027. A ranar 10 ga Oktoba ne dai ɗan takarar ya yi wa INEC ƙorafi kan rashin ganin sunan nasa acikin jaddawalin da ta wallafa.
Mohammed Haruna, wanda kwamishinan ƙasa ne na hukumar ya bayyana cewa an ɗauki ƙorafin Gwarzo a matsayin wanda ya yi nasara, saidai za a wallafa sunansa ne bayan fitar da sakamakon hukuncin Babbar Kotun Tarayya ta jihar Kano kan umarnin gaggawa da ta bayar game da matsalar.
Wani bincike da Manhaja ta yi, ya nuna cewa sunan Gwarzo da Mataimakinsa ba sa cikin jaddawalin da INEC ta sabunta, inda ta yi alama da cewa akwai batun izinin kotu a wajen da ta yi bayanin.
A ranar 27 ga Oktoba ne NDC ta garzaya Babbar Kotun Tarayya ta Abuja domin shigar da ƙorafin rashin ganin sunan ɗan takararta a jaddawalin ‘yan takarar gwamna da hukumar zaɓen ta fitar. A ciki ta nemi kotun ta umarci INEC ta sanya sunansa a jaddawalin.
Wasu rahotanni a ranar 29 ga Oktoba sun nuna cewa INEC ta amince da ƙorafin Gwarzo tare da na tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami na Jihar Gombe da na wasu ‘yan takara da da fari ba su ga sunayensu ba. Saidai ta ce ta yi haka ne bisa sakamakon da shari’o’in da ke kotuna za su nuna kan hukuncin nata.
Bayan cire suna Gwarzo da fari, an yi ta samun cece-kuce da kiraye-kirayen a warware batun daga ɓangaren NDC, wadda ta ce ɗan takarar nata ya cika dukkan sharuɗɗan da ake buƙata na shiga zaɓen.
