Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama wata mata mai shekara 18 mai suna Fatima Dalha bisa zargin caka wa mijinta, mai shekara 30, wuƙa a lokacin da suka yi saɓani a kan wasu kayanta a ƙaramar hukumar Dass ta jihar.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Nafiu Habib, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 6 na safiyar Lahadi, 25 ga Oktoba, 2026, a garin Lirr Bajar da ke ƙaramar hukumar Dass.
A cewar kakakin, saɓanin ya samo asali ne daga taƙaddama tsakanin ma’auratan kan wasu kayayyaki da kuɗin matar.
Ya ce Fatima ta fuskanci mijinta ne tana neman kuɗinta, zanenta da wayarta, waɗanda ta yi zargin suna hannunsa.
Sai dai taƙaddamar ta tsananta, har ta rikiɗe zuwa faɗa na zahiri. A yayin da suke artabu, ana zargin matar ta ɗauki wata wuƙa da ke kusa da su, ta caka wa mijinta a ciki.
Bayan faruwar lamarin, an garzaya da mijin zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci. Ya zuwa lokacin da aka fitar da rahoton, yana karɓar magani, kuma ba a tabbatar da cewa ya rasu ba.
Kakakin ’yan sandan ya aara da cewa ma’auratan ba su daɗe da yin aure ba, domin watanni kaɗan kawai suka yi da ɗaurin aurensu kafin faruwar wannan lamari.
Bayan harin, wasu fusatattun mutane sun taru a wurin, inda suka yi yunƙurin hukunta matar da kansu. Sai dai jami’an ’yan sanda daga ofishin ’yan sanda na Dass sun shiga tsakani, suka kuɓutar da ita daga hannun mutanen kafin su cutar da ita.
’Yan sandan sun kama matar tare da ƙwato wuƙar da ake zargin ta yi amfani da ita. An kuma bayyana cewa za a miƙa shari’ar zuwa sashen binciken manyan laifuka na rundunar ’yan sandan jihar domin gudanar da cikakken bincike.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, ya nuna damuwa kan yadda rikice-rikicen cikin gida ke ƙaruwa tsakanin matasa ma’aurata.
Ya buƙaci ma’aurata su riƙa warware saɓaninsu cikin lumana maimakon komawa ga tashin hankali.
Ya kuma yi gargaɗi ga jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu, yana mai jaddada cewa ya kamata a bar hukumomin da doka ta ba iko su gudanar da ayyukansu.
Rahoton ya nuna cewa lamarin ya sake jaddada muhimmancin haƙuri da tattaunawa wajen warware saɓanin aure, musamman a tsakanin ma’auratan da ba su daɗe da fara rayuwar aure ba.
