Sarkin Musulmi ya yi wa ‘ya’yansa biyu naɗin sarauta, Ɗan’iya, Oloyede da wasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar na III, ya bayar da muƙaman sarauta ga ‘ya’yansa biyu, wani sanannen mai taimakon al’umma, malami da wasu sanannun mutane. ‘Ya’yan sarkin sune, Abubakar Sadiq Abubakar da Shehu Usman Abubakar, waɗanda aka naɗa a matsayin Sarkin Dawaki Tsakar Gida da Fagachin Sakkwato, a wani biki da aka gudanar a Sakkwato, ranar Lahadi, 1 ga Nuwamba, 2026.

Haka kuma, an naɗa mai taimakon al’umma kuma malami, Alhaji Murtala Abdulƙadir Ɗan’iya a matsayin Dallatun Sakkwato da Farfesa Mansur Ibrahim a matsayin Ɗan-Masanin Sakkwato.

Sauran waɗanda aka yi wa naɗin sun haɗa da Alhaji Abubakar Hussain a matsayin Sarkin Bai; Alhaji Aminu Isa-Buhari a matsayin Ɗan-Malikin Sakkwato; Farfesa Ishaq Oloyede a matsayin Kuliyan Sakkwato; Dakta Peter Igoh a matsayin Kakakin Daular Usmaniyya; da Hon. Almustapha Rabah a matsayin Ɓauran Sakkwato.

Haka kuma, an naɗa Dakta Balarabe Kakale a matsayin Wakilin Makarantar Daular Usmaniyya; Alhaji Bello Abbas; Alhaji Gandi Umar a a matsayin Sarkin Galmar Sarkin Musulmi; da kuma Alhaji Abdulqadir Bello-Jeli a matsayinsa Sarkin Fulotin Sakkwato.

Da yake jawabi a taron, Sarki Sa’ad ya ce an yi waɗannan naɗe-naɗe ne bisa la’akari nagarta da gudunmawarsu ga al’umma da kuma nasarorin da suka cimma a rayuwa. Ya yi kira a gare su da su yi amfani da naɗe-naɗensu wajen hidima ga al’umma da kuma ɗaukar hakan a matsayin hanyoyin faɗaɗa nauye-nauyen da suka rataya a kansu. Kazalika, ya buƙaci su yi amfani da muƙaman nasu wajen tafiyar da lamuran zaman lafiya, haɗin kai da girmama addinan juna da ci-gaban Masarautar Kalifancin Sakkwato da ma Nijeriya baki ɗaya.

By Babaji

Leave a Reply