Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD
Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana yadda ya taɓa yin aikin tuƙin tasi a ƙasar Amurka domin samun kuɗin biyan kuɗin karatunsa, yana mai cewa wannan ƙwarewa ta taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa aniyarsa ta samar da damarmakin karatu ga yaran Nijeriya, ba tare da la’akari da matsayinsu na zamantakewa ko ƙarfin tattalin arzikin iyayensu ba.
Tinubu ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na ɗ a ranar Laraba, inda ya ce abubuwan da ya fuskanta a rayuwarsa sun taimaka wajen gina ƙudurinsa na ganin cewa kowane ɗan Nijeriya ya samu damar yin karatu bisa daidaito. Shugaban ƙasar ya ce, ya fahimci irin wahalhalun da ɗalibai ke fuskanta wajen biyan kuɗin makaranta da na masauki, kasancewar shi ma ya gamu da irin waɗannan ƙalubale a lokacin da yake karatu a Amurka.
A cewarsa, bayan isa Amurka yana matashi, ya dakatar da fara karatunsa na tsawon wasu watanni domin tara kuɗin da zai biya buƙatunsa na makaranta, kafin daga bisani ya koma birnin Chicago, inda ya gudanar da ayyuka daban-daban domin ɗaukar nauyin karatunsa na jami’a.
Ya ce, “A lokacin da na fara isa Amurka ina matashi, na yi aikin tuƙin tasi domin samun kuɗin karatuna. Har na kai ga jinkirta fara makaranta na wasu watanni domin in tara isassun kuɗaɗe. Bayan da na koma Chicago, na riƙa gudanar da ayyuka daban-daban domin ɗaukar nauyin kaina da biyan kuɗin karatuna na jami’a. Na san abin da yake nufi mutum ya riƙa damuwa kan kuɗin makaranta, masauki da yadda zai gudanar da rayuwarsa yayin da yake neman ilimi.”
Tinubu ya bayyana cewa ilimi na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta ba muhimmanci, inda ya bayyana cewa Asusun Ba da Lamunin Karatu na Nijeriya (NELFUND) ya bayar da lamunin kuɗi sama da naira biliyan 372 ga ɗalibai domin biyan kuɗaɗen makarantu da sauran buƙatun rayuwarsu. Ya kuma bayyana cewa ɗaliban kwalejojin fasaha na gwamnatin tarayya da wasu zaɓaɓɓun jihohi yanzu suna cin gajiyar karatu kyauta, tare da samun masauki, littattafan karatu da kayan makaranta ba tare da biyan kuɗi ba.
Shugaban ƙasar ya ƙara da cewa, shirin gwamnati na bunƙasa ilimin fasaha da koyon sana’o’i ya samu sama da aikace-aikacen neman shiga miliyan 2.8, yayin da aka gyara kwalejojin fasaha guda 38 a faɗin ƙasar.
Dangane da walwalar malaman jami’o’i da tabbatar da zaman lafiya a tsarin ilimin gaba da sakandare, Tinubu ya ce gwamnatinsa ta cimma sabuwar yarjejeniya da ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya (ASUU), wadda ta ƙunshi ƙarin kashi 40 cikin 100 na albashin malaman jami’o’i da kuma matakan da za su taimaka wajen tabbatar da ɗorewar zaman lafiya a jami’o’in ƙasar.
Ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa na ƙoƙarin ganin ɗalibai sun kammala karatunsu cikin wa’adin da aka tsara, ba tare da jinkirin da ba shi da dalili ba. Ya ce, “Karatun da aka tsara na tsawon shekaru huɗu, ya kamata a kammala shi cikin shekaru huɗu. Matasanmu sun cancanci kammala karatunsu a kan lokaci domin su ci gaba da rayuwarsu.”
Tinubu ya kuma bayyana cewa sama da yara miliyan ɗaya da a baya ba sa zuwa makaranta sun koma karatu, yayin da gwamnatinsa ke zuba jari wajen horas da malamai, faɗaɗa damar karatu ga ’yan mata da kuma aiwatar da sabon tsarin karatun ƙasa wanda ya dawo da koyar da tarihin Nijeriya a makarantu. Haka kuma, ya ce Gwamnatin Tarayya na kashe naira biliyan 110 wajen gyaran makarantun koyon aikin likitanci guda 24, yayin da adadin ɗaliban da ake ɗauka a kowace shekara domin karatun aikin jinya ya ƙaru daga 28,000 zuwa 115,000.
Ya ƙara da cewa, yawan ɗaliban da ake ɗauka domin karatun likitanci da likitan haƙora shi ma ya ƙaru daga 5,000 zuwa 12,000, yana mai cewa akwai buƙatar Nijeriya ta ƙara ƙarfin koyar da ƙwararrun ma’aikatan lafiya a cikin gida, maimakon dogaro da ƙasashen waje.
Shugaban ƙasar ya buƙaci ’yan Nijeriya da su yi amfani da wani dandali mai hulɗa da jama’a mai taken A zuwa Z, wanda Ma’aikatar Ilimi ta ƙasa ta samar domin wayar da kai kan Shirin Farfaɗo da Inganta Fannin Ilimi na Nijeriya.
Ya ce, dandalin zai taimaka wajen samar da bayanai kan shirye-shiryen gwamnati da damarmakin da iyaye, ɗalibai da malamai za su iya amfana da su. Ya kuma yi kira ga jama’a da su riƙa sanar da gwamnati matsalolin da ke addabar harkokin ilimi a yankunansu, yana mai cewa shawarwari da bayanan da jama’a ke bayarwa za su taimaka wajen gano giɓin da ke akwai da ɗaukar matakan magance su.
