Na haɗu da abokan karatun Tinubu da dama a Chicago, inji Alausa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya kare tarihin karatun Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Jami’ar Jihar Chicago da ke Amurka, inda ya dage cewa shugaban ƙasar ya kammala karatun digiri na farko a fannin lissafin kuɗi, wato Accounting, da sakamako mai daraja ta farko.

Alausa ya ce, yana da cikakken masaniya kan jami’ar, domin ya zauna a birnin Chicago na kusan shekaru 30, kuma ya taɓa haɗuwa da mutane da dama da suka yi karatu tare da Tinubu. Ministan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Talata, lokacin da ake tambayarsa game da takardun shaidar karatun shugaban ƙasa. Alausa ya ce, “Ina gaya muku tabbatattun bayanai ne. Na zauna a Chicago na kusan shekaru 30. Na ziyarci wannan jami’a sau da dama.”

Da aka tambaye shi ko ya taɓa haɗuwa da mutanen da suka yi karatu tare da Tinubu, sai ya amsa da cewa: “Tabbas, da dama sosai, kuma na haɗu da su ido-da-ido. Da yawa ƙwarai. Don haka a bar maganganun banza na cewa bai halarci jami’ar ba”

Haka kuma, lokacin da aka tambaye shi ko shugaban ƙasar ya kammala jami’ar da digiri mai daraja ta farko, ministan ya amsa da cewa: “A fannin lissafin kuɗi mana.” Ya kuma bayyana Tinubu a matsayin haziki na musamman, inda ya yi watsi da tambayoyin da ake yi kan ƙwarewar tunaninsa da fahimtarsa. “Tabbas, shi haziƙi ne. Kada ma mu fara magana kan ƙwarewar wannan shugaban ƙasa. Bola Ahmed Tinubu haziƙi ne na musamman,” inji shi.

Ministan ya kuma kare yadda Tinubu ke tafiyar da mulkin ƙasar, inda ya yi iƙirarin cewa shugaban ya sauya Nijeriya daga ƙasar da tattalin arzikinta ya durƙushe zuwa ƙasar da tattalin arzikinta ke samun bunƙasa. Alausa ya ce, “Ku duba yadda ya sauya ƙasar da ta kasance cikin mummunan halin tattalin arziki shekaru uku da suka gabata, zuwa ƙasar da tattalin arzikinta ke ci gaba da bunƙasa.”

Sai dai lokacin da mai tambayoyin ya ƙalubalanci wannan bayani, ta hanyar jawo hankalinsa kan yawan yaran da ba sa zuwa makaranta da kuma matsalar talauci a ƙasar, ministan ya dage cewa ya kamata a mayar da hankali kan nasarorin da shugaban ƙasar ya samu. “Ku bar ni na mayar da hankali kan abin da nake bayyanawa. Ba na son a karkatar da wannan tattaunawa. Amma wannan shugaban ƙasa ya samar wa Nijeriya da waɗannan nasarori,” inji shi.

Tarihin karatun Tinubu ya ci gaba da janyo cece-kuce a tsakanin al’umma, musamman bayan takaddamar da ta taso kan bayanan karatunsa na Jami’ar Jihar Chicago a lokacin shari’ar ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2023. An sake tayar da wannan batu a watan Agustan 2026, bayan da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta fara baje kolin bayanan sirri da takardun shaidar karatun ’yan takarar shugaban ƙasa na babban zaɓen 2027.

Takardar Tinubu mai lamba EC9, wadda jaridar PUNCH ta gani, ta nuna cewa ya samu digirin farko a fannin Gudanar da Kasuwanci (Business Administration) daga Jami’ar Jihar Chicago, inda aka ba shi shaidar kammala karatun a ranar 22 ga Yuni, 1979, tare da karramawa. Takardar ta kuma ƙunshi shaidar kammala hidimar bautar ƙasa (NYSC), wadda ta nuna cewa ya yi hidimar ne a Jihar Oyo daga watan Disamban 1982 zuwa Nuwamban 1983.

By ukarofi

Leave a Reply