A cigaba da gangamin yaƙin neman zaɓen Tinubu da Dikko na 2027, Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa ya isa ƙaramar hukumar Musawa inda ya kai ziyarar ban-girma ga Sarkin Gabas ɗin Katsina, Hakimin Jiƙamshi, Alhaji Abubakar Abdulmumini.
A yayin ziyarar, Gwamna Raɗɗa ya bayyana nasarorin gwamnatinsa a fannonin ilimi, kiwon lafiya, samar da ababen more rayuwa, noma da tsaro, inda ya bayyana cewa gina makarantun zamani, gyaran cibiyoyin kiwon lafiya, rarraba takin zamani a kowace shekara da samar da kayan aikin noma sun taimaka matuƙa wajen inganta rayuwar al’umma.
Ya danganta nasarorin da aka samu a matakin ƙananan hukumomi da aiwatar da ’yancin cin gashin kai na ƙananan hukumomi, tare da shirin Community Development Programme (CDP), wanda ke ƙarfafa al’umma ta hanyar tallafin noma, samar da kayan aikin ban-ruwa da shigar da sarakunan gargajiya cikin ayyukan ci gaba.
Haka kuma, Gwamnan ya jaddada samun gagarumin ci gaba a fannin tsaro a faɗin jihar, tare da bayyana ƙoƙarin gwamnatinsa na ƙarfafa sarautun gargajiya da na addini ta hanyar sauye-sauye da biyan alawus-alawus na wata-wata ga masu unguwanni da shugabannin addini.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC baya a babban zaɓen 2027.
A nasa jawabin, Hakimin Jiƙamshi ya yaba wa Gwamna Raɗɗa bisa ayyukan raya ƙasa, sauye-sauye da shirye-shiryen tallafa wa al’umma da gwamnatinsa ke aiwatarwa, musamman a fannonin ilimi, kiwon lafiya, noma da tsaro.
Ya kuma jinjinawa Gwamnan bisa damarmaki da shirye-shiryen ci gaba da aka samar wa al’ummar Jikamshi da ƙaramar hukumar Musawa baki ɗaya.
Daga baya Gwamnan ya kai ziyarar ban girma ga Sarkin Musawa Hakimin Musawa inda anan bayan koke da wani limamin yayi kan matsalar ruwan sha, Gwamnan Raɗɗa nan take ya bada umurnin gyara Dam na garin Musawa.
