’Yan kasuwa a Lafia sun koka kan tarin shara da ƙarancin tsaro

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

’Yan kasuwa a kasuwannin birnin Lafia, musamman Babban Kasuwar Zamani ta Lafia da ke Jihar Nasarawa, sun koka kan taɓarɓarewar tsafta, taruwar shara da kuma zargin sakaci daga Hukumar Kula da Kasuwannin Jihar Nasarawa.

’Yan kasuwar sun bayyana cewa gwamnati ta yi watsi da su, inda suka ce kasuwannin na fama da tarin shara, lalacewar hanyoyin shiga, ƙarancin tsaro da kuma rashin muhimman abubuwan more rayuwa, ciki har da ruwan sha.

ɗaya daga cikin ’yan kasuwar, Sule Ali, ya ce halin rashin tsaftar da ake ciki a Babbar Kasuwar Zamani ta Lafia na jefa lafiyar jama’a cikin haɗari, don haka ya buƙaci gwamnati ta gaggauta ɗaukar matakin magance matsalar.

Ali ya bayyana cewa rashin kwashe shara da ragowar abinci a kan lokaci na jawo kwari da beraye, lamarin da ke iya yaɗa cututtuka tare da jefa ’yan kasuwa da masu sayayya cikin barazanar kamuwa da cututtuka.

Ya yi zargin cewa ana barin sharar da ya kamata a riƙa kwashewa duk bayan kwana biyu ko kuma mako guda, har na tsawon watanni ba tare da an kai ga kwashe ta ba.

A cewarsa, ’yan kasuwar da shagunan su ke kusa da wurin zubar da shara na fuskantar asarar kuɗi saboda raguwar kwastomomi, sakamakon wari da ke hana mutane zuwa sayayya a yankin.

Ya zargi Hukumar Kula da Kasuwannin Jihar Nasarawa da gaza magance ƙorafe-ƙorafen da suke gabatar mata.

Haka kuma, Shugaban Babbar Kasuwar Zamani ta Lafia, Muhammad Nureedeen, ya zargi hukumar da karɓar haraji da kuɗaɗen caji fiye da kima, alhali ba ta samar musu da ayyukan da suka dace da kuɗin da take karɓa.

Ya ce, ’yan kasuwa na ci gaba da biyan kuɗaɗen hidima, amma ba sa samun ayyukan da suka yi daidai da abin da suke biya.

Nureedeen ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta mayar da alhakin karɓa da kula da kuɗaɗen hidimar kasuwa hannun shugabancin kasuwar, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen inganta ayyukan da ake samar wa ’yan kasuwa.

Ya kuma nuna damuwa kan yadda rashin kwashe shara a kai a kai zai iya ƙara haɗarin yaɗuwar cututtuka, musamman waɗanda ke da alaƙa da rashin tsafta, kamar kwalara da zazzaɓin typhoid.

“Idan kasuwa ta kasance mai tsafta, masu sayayya za su ji daɗin zuwa, harkokin kasuwanci su bunƙasa, kowa kuma ya rayu cikin ƙoshin lafiya. Kasuwa mai tsafta na nufin al’umma mai ƙoshin lafiya,” inji shi.

Baya ga matsalar tsafta, Nureedeen ya ce rashin bankuna a cikin kasuwar da kewayenta na ƙara jefa ’yan kasuwa cikin fargaba ta fuskar tsaro, musamman ganin cewa suna riƙe da kuɗaɗen da suke samu daga cinikin yau da kullum.

Shi ma Shugaban ƙaramar Kasuwar Unguwar Lafia, Yusuf Rabi’u, ya ce ’yan kasuwa na yawan damuwa kan tsaron kayayyakinsu, musamman bayan an rufe kasuwa da yamma.

Ya ce biyan kuɗin tsaro zai iya taimakawa wajen inganta tsaron kasuwannin, matuƙar ana yin cikakken bayani kan yadda ake amfani da kuɗin tare da tabbatar da cewa an kashe shi a kan abin da aka tara shi dominsa.

Rabi’u ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Nasarawa da ta ƙarfafa tsaro a kasuwannin tare da hana tilasta wa ’yan kasuwa biyan wasu kuɗaɗen da ba su dace ba.

Da yake mayar da martani kan ƙorafe-ƙorafen, Babban Daraktan Hukumar Kula da Kasuwannin Jihar Nasarawa, Yakubu Ahmed Ubangari, ya tabbatar wa ’yan kasuwar cewa hukumar za ta ƙara ƙaimi wajen magance matsalolin da suka gabatar.

Dangane da kuɗaɗen hidima kuwa, Ubangari ya bayyana cewa kuɗin da ake karɓa daga ’yan kasuwa bai wadatar wajen biyan dukkan buƙatun kasuwannin ba, waɗanda suka haɗa da kwashe shara, biyan jami’an tsaro da kuma sauran ayyukan gyara da kula da muhalli.

“Kuɗin hidimar da suke magana a kai ba wani abu ne mai yawa ba. Kuɗin kaɗan ne ƙwarai. Suna biyan tsakanin naira 9,000 zuwa 12,000 a shekara. Ta yaya za a yi tsammanin wannan kuɗi zai iya ɗaukar nauyin dukkan ayyukan da ake buƙata? Ba zai yiwu ba. Amma muna ƙoƙarin ganin mun samar musu da ayyukan da suka dace,” inji shi.

Sai dai Babban Daraktan ya yi alƙawarin isar da ƙorafe-ƙorafen ’yan kasuwar ga gwamnatin jihar domin neman ɗaukar matakan magance wasu daga cikin matsalolin tsaro.

Ya ce hukumar za ta buƙaci gwamnati ta ɗauki nauyin biyan albashin wasu daga cikin jami’an tsaron kasuwannin, ta hanyar shigar da su cikin tsarin biyan albashin ma’aikatan gwamnati.

A cewarsa, hakan zai ba hukumar damar ƙara alawus ɗin sauran jami’an tsaron tare da karkatar da kuɗaɗen da ake da su zuwa magance sauran matsalolin da suka addabi kasuwannin.

By ukarofi

Leave a Reply