Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, tare da Shugaban Kwamitin Kwastam na Majalisar Wakilai, Hon. Leke Joseph Abejide, sun jagoranci gangamin wayar da kan al’ummar Yarabawa da sauran ƙabilun da ba ’yan asalin Jihar Kano ba, domin su mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya wajen neman wa’adi na biyu, tare da goyon bayan sake zaɓen Gwamna Abba Yusuf a zaɓen shekarar 2027.
Gangamin ya gudana ne a yayin wani shirin tallafa wa jama’a da Hon. Abejide ya shirya. Shi ne wakilin mazabun Yagba West, Yagba East da Mopa-Muro a Jihar Kogi. A yayin taron, ya sanar da ware tallafin kuɗi har Naira miliyan 500 domin bunƙasa sana’o’in matan Yarabawa da ke zaune a Jihar Kano.
Abejide, wanda ya bayyana cewa ya shafe sama da shekaru 30 yana zaune a Kano, ya bayyana jihar a matsayin gidansa na biyu. Ya ce mafi yawan dukiyarsa da nasarorin da ya samu sun samo asali ne daga Kano, kafin ya shiga harkokin siyasa.
A wani mataki na nuna jajircewarsa wajen tallafa wa mutanen da ba ’yan asalin jihar ba, ɗan majalisar ya kuma raba kayan abinci, tufafi da sauran kayayyakin amfanin gida ga al’ummomi daban-daban, ciki har da mutanen Igala, Ebira da Bassa.
Ya bayyana cikakken goyon bayansa ga Shugaba Tinubu, Gwamna Abba Yusuf da sauran ’yan takarar jam’iyyar APC a zaɓe mai zuwa, inda ya buƙaci waɗanda suka amfana da tallafin da ya bayar su rama wannan alheri ta hanyar ba su goyon baya da ƙuri’unsu.
Abejide ya yi alƙawarin dawowa da wasu shirye-shiryen tallafa wa jama’a idan waɗanda suka amfana suka ci gaba da nuna goyon baya. Ya bayyana cewa shirin tallafinsa na gaba zai mayar da hankali ne kan al’ummar Hausawa da Fulani da ke ƙaramar Hukumar Nasarawa.
A nasa jawabin, Gwamna Abba Yusuf ya yi kira ga sauran ’yan Majalisar Dokoki ta ƙasa da su yi koyi da Hon. Abejide ta hanyar tallafa wa al’ummominsu da sauran ’yan Nijeriya, ba tare da la’akari da bambancin ƙabila ko addini ba, domin ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, wanda ya halarci taron, ya bayyana cewa sake zaɓen Shugaba Tinubu da Gwamna Abba Yusuf na da matuƙar muhimmanci ga al’ummar da ba ’yan asalin Kano ba, bisa la’akari da ayyukan raya ƙasa da gwamnatin tarayya ta kawo jihar, da kuma manyan ayyukan more rayuwa da gwamnatin Kano ke gudanarwa.
ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da suka fi ɗaukar hankali a taron shi ne ƙaddamar da shirin tara Naira biliyan uku domin gina sabon katafaren fadar Oban Yarabawa ta zamani a Jihar Kano.
Hon. Abejide ya bayar da gudummawar Naira miliyan 220 ga wannan aiki, yayin da wasu abokan hulɗarsa guda biyu suka bayar da gudummawar Naira miliyan 200 da Naira miliyan 500, bi da bi. Haka kuma, Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da gudummawar Naira miliyan 100 domin tallafa wa aikin.
Taron ya samu halartar shugabannin siyasa, wakilan sarakunan gargajiya da kuma mambobin al’ummar Yarabawa da sauran ƙabilun da ba ’yan asalin Kano ba, lamarin da ke nuna ƙoƙarin haɗa kan al’ummomi daban-daban domin samun goyon bayan siyasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
