Daga AISHA ASAS
Tsohuwar jarumar fina-finan batsa kuma mai tasiri a kafafen sada zumunta, Cindy Oshodi, ta bayyana yadda abubuwan da suka faru a rayuwarta a baya ke ci gaba da damunta, inda ta fashe da kuka yayin da take magana kan nadamar da take ciki da kuma halin kaɗaicin da ta ce take fuskanta a yanzu.
Cindy ta bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da ta wallafa a shafinta na TikTok, inda ta bayyana cewa ta kai matsayin da wani lokaci take fatan ta ɓace daga duniya saboda gajiyar rayuwa da kuma yadda abubuwa suka sauya mata.
A cikin bidiyon, wanda ta kasa riƙe hawayenta ta ce tana jin kamar ba ta da mutanen da za ta kira abokai na gaskiya, domin kuwa ko waɗanda take ganin suna tare da ita, a cewarta, ba sa nuna mata sahihiyar ƙauna.
Ta ce: “Abin da nake fata kawai shi ne in tafi, in yi barci kuma wataƙila kada in sake farkawa, saboda na gaji. Ina fatan da na yi rayuwata yadda ya kamata. Babu wanda yake son ya zama abokina. Ko da ina da abokai, na kan tarar ba na gaskiya ba ne.”
Cindy ta kuma bayyana cewa ‘yarta ce babban abin da ke ƙarfafa ta wajen ci gaba da rayuwa, duk da irin matsin lambar da take fuskanta.
A kalamanta, ta ce wani lokaci tana jin kamar ta kawo ƙarshen rayuwarta, amma idan ta tuna da ‘yarta sai ta sake samun dalilin da zai sa ta ci gaba da rayuwa.
Da take magana kan abubuwan da suka faru a baya, Cindy ta bayyana nadamar da take ji, inda ta ce tana fatan da ba ta aikata wasu abubuwan da suka shafi rayuwarta ba.
Ta ce: “Na rasa rayuwata. Ina nadamar duk abin da na yi wa rayuwata. Da ma ba a haife ni ba. Da ma ban aikata waɗancan abubuwan ba. Abin da nake fata kenan kawai.”
A wani ɓangare na bayaninta, tsohuwar jarumar ta yi maganganun da suka ƙara tayar da hankalin masu bibiyarta, inda ta nuna cewa idan har ta kai matsayin da za ta yanke shawarar kashe kanta, ba za ta sanar da kowa ba.
Ta ce idan har masu bibiyarta suka daina ganinta a kafafen sada zumunta, su ɗauka cewa wani abu ya faru da ita.
Wannan furuci ya ƙara jawo hankalin jama’a kan irin halin da take ciki, musamman yadda ta bayyana cewa tana jin tsoron kaiwa wani matsayi da ba za ta iya jurewa halin da take ciki ba.
Bayan bayyanar bidiyon, mutane da dama sun bayyana ra’ayoyinsu a kafafen sada zumunta, inda wasu suka yi mata nasiha tare da ƙarfafa mata gwiwa da kada ta bari abubuwan da suka faru a baya su hana ta sake gina rayuwarta.
Wasu daga cikin masu sharhi sun bukace ta da ta koma ga Allah, ta nemi gafara, tare da fara sabon babi na rayuwa, yayin da wasu suka nuna damuwarsu kan kalaman da ta yi game da tunanin kashe kanta.
Sai dai wasu kuma sun yi amfani da damar wajen sukar abubuwan da suka shafi rayuwarta a baya, inda suka bayyana cewa wasu zaɓuɓɓukan rayuwa kan zo da sakamakon da mutum zai iya fuskanta bayan lokaci.
Lamarin ya sake buɗe tattaunawa kan yadda abubuwan da mutum ya aikata a baya za su iya ci gaba da shafar rayuwarsa, musamman idan suka kasance abubuwan da suka bazu a kafafen sada zumunta.
