Gombe ta tsaurara matakan kula da shanu don kare gonakin manoma har zuwa 2027

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

Gwamnatin Jihar Gombe ta umarci kwamitocin da ke kula da sasanta rikice-rikicen manoma da makiyaya a ƙananan hukumomi 11 na jihar da su ƙara ƙaimi wajen sanya ido da kuma taƙaita zirga-zirgar shanu ta hanyoyin shiga da aka ware, har zuwa ƙarshen watan Janairun 2027.

Matakin na da nufin kare gonakin manoma daga lalacewa, daƙile rikice-rikice da kuma tabbatar da gudanar da girbin amfanin gona cikin kwanciyar hankali a faɗin jihar.

Shugaban kwamitin sasanta rikice-rikicen manoma da makiyaya na jihar, Alhaji Abdulkadir Mohammad, ne ya bayar da wannan umarni yayin wani taron ganawa da manema labarai a Gombe.

Mohammad, wanda shi ne kwamishinan ma’aikatar aikin gona da kiwo, ya ce umarnin na cikin ƙoƙarin gwamnati na ƙarfafa nasarorin da kwamitin ya samu ta hanyar wayar da kan sarakunan gargajiya da shugabannin ƙananan hukumomi.

Ya bayyana cewa an shirya taron ne domin sanar da jama’a irin nasarorin da kwamitin ya samu, ƙalubalen da ya fuskanta yayin tattaunawa da masu ruwa da tsaki, da kuma matakan da ake ɗauka domin hana sake samun arangama tsakanin manoma da makiyaya.

Kwamishinan ya gargaɗi makiyaya da su guji kiwo da daddare, tare da hana barin yara ƙanana su kula da shanu, yana mai cewa irin waɗannan halaye na iya ƙara tayar da hankali da haddasa rikice-rikicen da za a iya kauce musu.

Haka kuma, ya buƙaci manoma da su daina ƙona ragowar amfanin gona bayan girbi, tare da guje wa jigilar amfanin gonakinsu da daddare, yana mai gargaɗin cewa duk wanda aka samu ya karya dokokin da suka shafi waɗannan ayyuka zai fuskanci hukuncin da ya dace.

Mohammad ya kuma yi kira ga manoma da makiyaya da kada su ɗauki doka a hannunsu, maimakon haka su riƙa kai rahoton duk wani motsi ko abin da suka zargi da tayar da hankali ga jami’an tsaro mafi kusa ko hukumomin da abin ya shafa domin ɗaukar matakin gaggawa.

Ya bayyana cewa tsaro nauyin kowa ne, yana mai jaddada cewa nasarar ƙoƙarin gwamnati na hana rikice-rikice ya ta’allaka ne da haɗin kan al’umma da sauran masu ruwa da tsaki.

Shugaban kwamitin ya yaba wa sarakunan gargajiya da shugabannin ƙananan hukumomi bisa gudummawar da suke bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya, tare da kira gare su da su ci gaba da wannan goyon baya.

Ya kuma gode wa Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, bisa ci gaba da tallafa wa kwamitin wajen gudanar da ayyukansa.

Mohammad ya sake jaddada aniyar kwamitin na ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin manoma da makiyaya, kare harkokin noma da kuma tabbatar da cewa an gudanar da girbin amfanin gona ba tare da wata tangarɗa ba a faɗin jihar.

By ukarofi

Leave a Reply